Badakalar N369m: Sanata Hunkuyi ya ki amsa gayyatar yan sanda, sun bazama nemanshi

Badakalar N369m: Sanata Hunkuyi ya ki amsa gayyatar yan sanda, sun bazama nemanshi

- Hukumar yan sanda sun bazama neman sanata Hunkuyi

- An nemeshi an rasa tun lokacin da hukumar yan sanda ta gayyaceshi

Legit.ng Sanata Suleiman Hunkuyi mai wakiltan Kaduna ta Arewa ya ki amsa goron gayyatan da hukumar yan sanda sukayi masa kan binciken badakalar N369 million.

Hukumar yan sanda ta mika sakon gayyata ga Hunkuyi da shugaban kungiyar kwadagon jihar Kaduna, Mr Adamu Ango domin bayani da kan rawar da suka taka kan wani aikin fili.

Yayinda Mr Adamu Ango ya amsa gayyatar, har yanzu Sanata Hunkuyi bai bayyana gaban sifeto janar na hukumar dake Abuja ba.

KU KARANTA: Angela Merkel ta iso Najeriya

An gayyaci Sanatan domin ya tattauna da ACP Sanusi Mohammed a madadin mataimakin kwamishanan yan sandan rundunar IGP na yan sanda.

Duk kafafen samun neman a kulle suke yayinda manema labarai sukayi kokarin tuntubarsa kan wannan zargi da hukumar yan sanda ke masa.

Wani babban jami’an yan sanda da yayi magana kan al’amarin jiya yace: “A kwanaki 27 da suka gabata, mun kasance muna sauraron Sanata Hunkuyi. Mun bi shi har gidansa da ke Kaduna a karshen makon da ya gabata amma bamu sameshi ba.”

“Bibiyanshi ya yi wuya saboda lambobin da yake amfani da su basu shiga, har da wani na kasar Benin ya kashe.”

“Idan bai bayyana ba, hukumar yan sanda za ta alanta nemanshi ruwa a jallo.”

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel