Abinda ya sa muke da tabbas din lashe zaben gwamna a Osun - Jam'iyyar APC

Abinda ya sa muke da tabbas din lashe zaben gwamna a Osun - Jam'iyyar APC

- Jam'iyyar APC ba bayyana tabbacin cewa ita za tayi nasara a zaben gwamna mai zuwa na jihar osun

- Shugaban jam'iyyar na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ne ya ce babu shakka dan takarar jam'iyyar, Isiaka Adegboyega Oyetola, shine zai lashe zaben

- Tinubu ya ce Oyetola yana daya daga cikin kwararu da su kafi cacanta da mulkin jihar ta Osun

Punch ta ruwaito cewa shugaban jam'iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ne ya ce jam'iyyarsu tana da ikon lashe zaben gwamna da za'a gudanar a ranar 22 ga watan Satumba a jihar Osun.

Tinubu ya yi wannan maganar ne yayin da yake zantawa da manema labarai bayan taron da shuganin jam'iyyar APC na yankin kudu maso yamma suka yi da shugaba Muhammadu Buhari a Aso Villa a jiya 30 ga watan Augustan 2018.

Abinda ya sa muke da tabbas din lashe zaben gwamna a Osun - Tinubu

Abinda ya sa muke da tabbas din lashe zaben gwamna a Osun - Tinubu
Source: Depositphotos

Masu ruwa da tsakin na yankin kudu maso yamma sunyi amfani da wannan damar don gabatar da dan takarar gwamna a jam'iyyar, Alhaji Isiaka Adegboyega Oyetola ga shugaba Muhammadu Buhari.

DUBA WANNAN: Buhari, Tinubu da shugabanin APC na kudu maso yamma sun saka labule a fadar Aso Villa

Tinubu ya ce dimbin ayyukan alkhairi da gwamna mai barin gado, Rauf Aregbesola, ya shimfida a jihar zai taimaka wajen bawa jam'iyyar nasara. Ya kara da cewa ayyuka na gari daa Oyetola ya gudanar a wuraren da ya yi aiki a baya shima zai taimaka sosai.

Kalaman Tinubu: "Muna sa ran samun nasara. Gwamna mai barin gado dan jam'iyyar mu ne kuma ya shimfida ayyuka na gari. Muna sa ran zamu samu damar daurawa daga inda ya tsaya.

"Kazalika, mun zakulo daya daga cikin 'yan takara mafi cacanta a jihar mai suna Alhaji Isiaka Adegboyega Oyetola. Yana da kwarewa wajen aiki sosai."

A bangarensa, Oyetola ya mika godiyarsa ga deleget din jam'iyyarsa, inda ya kara da cewa zai yi nasara a zaben. Ya ce: "Wannan ziyarar ta nuna cewa shugaban kasa na kowa ne. Ya dukufa wajen ganin APC tayi nasara a zaben ranar 22 ga watan Satumba."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel