Zan cigaba da kasancewa a majalisar dattawa har abada idan na so - Ekweremadu

Zan cigaba da kasancewa a majalisar dattawa har abada idan na so - Ekweremadu

- Mataimakin shugaban majalisar dattawa yace yana iya kasancewa a majalisa muddin rayuwarsa idan har yayi muradin aikata hakan

- Ekweremadu yace a ko da yaushe yana tuntubar al'umman mazabarsa

- Yace sirrin dadewa a siyasa shine kasancewa tare da al'ummanka a ko da yaushe

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu yayi ikirarin cewa yana iya cigaba da kasancewa a majalisar dattawa iya tsawon rayuwarsa idan har ya so hakan.

Mista Ekweremadu yace a ko da yaushe yana tuntubar mazabarsa, kuma yana iya zin zabe cikin sauki.

Ya bayyana hakan a ranar Alhamis, 30 ga watan Agusta a otel din Sheraton a wani taron tattaunawa da kungiyar matasan #NotTooYoungToRun suka shirya akan rage shekarun takara da aka rage a fadin siyasar kasar.

Zan cigaba da kasancewa a majalisar dattawa har abada idan na so - Ekweremadu

Zan cigaba da kasancewa a majalisar dattawa har abada idan na so - Ekweremadu
Source: Depositphotos

Ekweremadu ya bukaci yan takara da su dunga kasancewa tare da yan mazabarsu a koda yaushe, cewa ta hakan ne kawai mutun zai cigaba da taka rawar gani a siyasa.

Har ila yau a wajen taron ne shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya bayyana kudirinsa na son tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zabe mai zuwa.

KU KARANTA KUMA: Ku sake zaba na a matsayin shugaban kasa a 2019 – Buhari ya roki mata

A baya Legit.ng ta rahoto cewa, a kokarin ganin an gabatar da zaben fidda gwani na gaskiya da amana, shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na kasa ya gana da ‘yan takarar kujerar shugaban kasa a Abuja a daren ranar Laraba, 29 ga watan Agusta.

Tawagar ta jam’iyyar PDP sun samu jagorancin shugaban jam’iyyar na kasa, Prince Uche Secondus.

Sauran mambobin da suka halarci wannan ganawar sun hada da kwamitin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar na kasa da wasu mambobin kungiyar amintattu na jam’iyyar.

Wadanda suka halarci ganawar sun hada da Shugaban majalisar dattawa, Dr Bukola Saraki, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, tsohon gwamnan jihar Plateau, Jona Jang, Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa da kuma tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Ahmed Makarfi.

Hakazalika tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso da tsohon ministan ayyuka na musamman, Alhaji Kabir Tanimu Turaki sun hallara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel