Sanata Akpabio da Ministoci 9 na cikin tawagar Shugaba Buhari zuwa Kasar Sin

Sanata Akpabio da Ministoci 9 na cikin tawagar Shugaba Buhari zuwa Kasar Sin

A yayin da rahotanni suka bayyana cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari zai shilla zuwa Birnin Sin watau 'Kasar China a ranar yau ta yau Juma'a, mun samu cewa akwai kimanin Sanatoci hudu da za su yi wannan dogon tattaki cikin tawagar ta shugaban kasa.

A ranar Alhamis din da ta gabata ne kakakin shugaban kasa, Mallam Garba Shehu, ya bayyana cewa shugaba Buhari zai yi bankwana da birnin Abuja a yau Juma'a zuwa birnin Sin domin halartar taron hadin kan kashashen biyu.

Shugaba Buhari zai halarci wannan babban taro kan hadin kan kasar Najeriya da kuma China karo na bakwai da za gudanar a ranar 3 da kuma 4 ga watan Satumba.

Kamar yadda kakakin shugaban kasar ya bayyana, shugaba Buhari yayin isarsa zai halarci taron zama na sauraron ra'ayoyin al'ummar Najeriya a ofishin jakadancin kasar nan dake Birnin na China.

Sanata Akpabio da Ministoci 9 na cikin tawagar Shugaba Buhari zuwa Kasar Sin

Sanata Akpabio da Ministoci 9 na cikin tawagar Shugaba Buhari zuwa Kasar Sin
Source: Depositphotos

Rahotanni sun bayyana cewa, baya ga Sanatoci hudu akwai kuma Ministoci 9 na shugaba Buhari da za su shiga wannan babbar tawaga da suka hadar da; Geofferey Onyeama, Rotimi Amaechi, Muhammad Bello, Okechukwu Enelamah, Udoma Udo Udoma, Suleiman Adamu, Ibe Kachikwu da kuma Hadi Srika.

Sanatocin sun hadar da; Godswill Akpabio, Abdullahi Adamu, George Akume da kuma Aliyu Magatakarda Wamakko.

KARANTA KUMA: Ziyarar Theresa May ta ƙarfafa dangartaka tsakanin 'Kasar Birtaniya da Najeriya

Tawagar ta shugaban kasa ta kuma hadar da gwamnonin wasu jihohi; Muhammadu Abdullahi, Akinwunmi Ambode, Muhammad Badaru Abubakar da kuma Rochas Anayo Okorocha.

Sauran 'yan tawagar sun hadar da; mai bayar da shawara kan harkokin tsaro na kasa; Babagana Monguno, shugaban hukumar NIA; Ahmed Abubakar da kuma shugaban kamfanin man fetur na kasa; Maikanti Baru.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit

Mailfire view pixel