Zabukan 2019: Hafsan hafsoshin Najeriya ya aike da zazzafan gargadi ga 'yan siyasa

Zabukan 2019: Hafsan hafsoshin Najeriya ya aike da zazzafan gargadi ga 'yan siyasa

- Hafsan hafsoshin Najeriya ya aike da zazzafan gargadi ga 'yan siyasa

- Yace dole ne suyi taka tsantsan da kalaman su

- Yace ba za su zura masu ido ba su tada tarzoma

Hafsan hafsoshin tsaron Najeriya Janar Abayomi Olanisakin ya gargadi 'yan siyasar kasa da babbar murya game da neman tada zaune-tsaye a kafin, lokacin da kuma bayan zabukan gama gari da za'a gudanar na shekarar 2019.

Zabukan 2019: Hafsan hafsoshin Najeriya ya aike da zazzafan gargadi ga 'yan siyasa

Zabukan 2019: Hafsan hafsoshin Najeriya ya aike da zazzafan gargadi ga 'yan siyasa
Source: UGC

KU KARANTA: Jiragen ruwa 13 sun kawo kaya Najeriya

Janar Olanisakin ya yi wannan gargadin ne a garin Sokoto inda yaje domin kaddamar da wani sansanin soji na kai agajin gaggawa a barikin sojojin Sama na 119 a kasar dake can garin.

Legit.ng haka zalika ta tsinkaye shi yana ba 'yan siyasar shawara da cewa su bi hanyoyin sulhu wajen sasanta tsakanin su a maimakon yin tashin tashina da zata jefa rayukan al'umma cikin matsanancin hali.

Shima dai yake jawabin sa, shugaban hukumar kai agajin gaggawa ta kasa da ya samu wakilcin babban daraktan hukumar, ya bukaci hadin kan al'umma domin samun zaman lafiya dawwamamme.

A wani labarin kuma, Fitaccen marubucin nan kuma wanda ya taba lashe kambun Laureate, Farfesa Wole Soyinka a ranar Alhamis din da ta gabata ya soki Shugaba Buhari a game da ikirarin da yayi na cewa zaman lafiyar kasa yafi bin dokokin ta muhimmaci a wurin sa.

Shugaba Buhari din dai ya yi wannan ikirarin ne a cikin jawabin sa na musamman da ya gabatar a wajen babban taron kungiyar lauyoyin Najeriya da suka gabatar a garin Abuja, babban birnin tarayya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel