Rashawa: EFCC ta taso wani Sanatan jam'iyyar PDP a gaba

Rashawa: EFCC ta taso wani Sanatan jam'iyyar PDP a gaba

- EFCC ta taso wani Sanatan jam'iyyar PDP a gaba

- Sanatan dai shi kadai ne bai koma APC ba a jihar Akwa Ibom

- Ana zargin sa da karbar cin hancin motocin Naira miliyan 254

Hukumar nan ta gwamnatin tarayya dake yaki da masu yiwa tattalikin kasa zagon kasa watau EFCC a takaice ta shigar da kara a wata babbar kotu dake a garin Legas akan wani Sanata daga jihar Akwa Ibom game da almundahana ta wasu makudan kudade.

Rashawa: EFCC ta taso wani Sanatan jam'iyyar PDP a gaba

Rashawa: EFCC ta taso wani Sanatan jam'iyyar PDP a gaba
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Wani malamin izala ya cinye kudin ginin masallaci a Kano

Kamar yadda muka samu Sanatan mai suna Albert Bassey EFCC na tuhumar sa ne da laifin ansar cin hancin motoci 12 da kudin su ya kai Naira miliyan 254 daga hannun wani dan kasuwa a lokacin yana kwamishinan kudi a jihar ta Akwa Ibom.

Legit.ng ta samu cewa yanzu haka dai Sanata Albert Bassey shi kadai ne ya rage a jam'iyyar PDP a jihar biyo bayan ficewar sauran biyu da suka hada da Sanata Godswill Akpabio da kuma Nelson Effiong da suka koma APC a kwanan baya.

A wani labarin kuma, Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma dan takarar neman tikitin shugaban kasar Najeriyar a karkashin inuwar jam'iyyar PDP a zabe mai zuwa na 2019 watau Atiku Abubakar ya fadi ta cikin sa game da abunda zai yi idan har ya rasa tikitin takarar jam'iyyar.

Fitaccen dan siyasar yace tabbas zai taimaka da dukkan damar da Allah ya bashi don ganin jam'iyyar ta sa tayi nasara koda bai samu tikitin takarar ta ba idan dai har aka yi adalci wajen zaben.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel