Mun fitar da ýan Najeriya daga kangin talauci - Osinbajo

Mun fitar da ýan Najeriya daga kangin talauci - Osinbajo

- Mataimakin shugaban kasa ya ce gwamnatin Buhari ta fitar da miliyoyin al'umman kasar daga kangi na talauci

- Osinbajo yayi martani ne ga ikirarin Theresa May na cewa Najeriya na da mafi yawan matalauta

- Ya sha alwashin cewa gwamnati zata zuba jari akan ýan Najeriya sannan ta basu ingantaccen rayuwa

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa gwamnatin Shugabna kasa Muhammadu Buhari ta fitar da miliyoyin ýan Najeriya daga kangin talauci a shekaru uku da suka gabata.

Yana martani ne akan jawabin da Firai Minista Theresa May da tace kasar Najeriya ce ke da matalauta mafi yawa.

Mun fitar da ýan Najeriya daga kangin talauci - Osinbajo

Mun fitar da ýan Najeriya daga kangin talauci - Osinbajo
Source: Depositphotos

Osinbajo yace a wannan lokaci, gwamnatin ta zuba tushe mai karfi domin inganta tattalin arziki, samar da ababen more rayuwa da kuma bayar da dama ga hukumomi masu zaman kansu domin ci gaba ta hanyar shirin farfado da tattalin arziki.

Mataimakin shugaban kasar, wanda yayi magana a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, a taron kungiyar tsare-tsaren ci gaba (NCPD) karon na 17 ya bayyana shirin zuba jari a matsayin abunda akayi amfani da su wajen fitar da miliyoyin ýan Najeriya daga kangin talauci.

KU KARANTA KUMA: PDP ta bukaci Tambuwal, Atiku, Kwankwaso da sauransu da su amince da duk sakamakon da zaben fidda gwani ta fitar

Ya samu wakilin Ministan kasafin kudi da tsare-tsare, Sanata Udoma Udo Udoma.

Osinbajo yace gwamnati zata zuba jari a ýan Najeriya sannan ta basu ingantaccen rayuwa .

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel