Zaɓen APC a 2019 zai kara raba Najeriya - Lamido

Zaɓen APC a 2019 zai kara raba Najeriya - Lamido

Za ku ji cewa a ranar Alhamis din da ta gabata ne tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma manemin takarar kujerar shugaban kasa karkashin inuwa ta jam'iyyar PDP, Alhaji Sule Lamido, ya bayyana abinda zaben jam'iyyar APC zai haifar a kasar nan.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, tsohon gwamnan ya yi gargadin cewa muddin aka tabbatar da nasarar jam'iyyar APC a zaben 2019 to kuwa ba bu shakka hakan zai kara raba kan Najeriya.

Lamido ya bayyana hakan ne yayin jaddada kudirin sa na takarar shugaban kasa a zaben 2019 ga mambobin jam'iyyar yayin da ya kai ziyarar ban girma ga gwamnan jihar Benewe, Samuel Ortom.

Tsohon ministan na harkokin kasashen ketare ya bayyana cewa, jam'iyyar APC ta kawo wata mummunar akida mai cike da guba da kuma dafi na rabuwar kai da manufa ta yaudarar al'ummar kasar nan.

Zaɓen APC a 2019 zai kara raba Najeriya - Lamido

Zaɓen APC a 2019 zai kara raba Najeriya - Lamido
Source: Depositphotos

A cewar sa, akwai raunin zuciya a tattare da wasu 'yan siyasa dake sauya sheka zuwa jam'iyyar APC domin neman mafaka da kariya ta samun wurin zama.

KARANTA KUMA: Cikin Hotuna: Shugaba Buhari ya halarci taron Jiga-Jigan jam'iyyar APC

Ya ci gaba da cewa, jam'iyyar APC na ci gaba da yada wata farfaganda dake janyo salwantar rayuka da zubar jinin al'umma tare da rashin samun sukuni na zaman lafiya da ta'addanci ya janyo a kasar nan.

A yayin haka jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, a ranar da ta gabata ne aka gudanar da taron kusoshin jam'iyyar APC inda ta sha alwashin tabbatar da gaskiya da adalci yayin zaben 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel