Mai kan uwa da wabi: Yan bindiga sun bindige Yansanda biyu, direba a jihar Ribas

Mai kan uwa da wabi: Yan bindiga sun bindige Yansanda biyu, direba a jihar Ribas

Wasu gungun masu garkuwa da mutane sun kai farmaki akan wani farar fata a garin Woji dake cikin karamar hukumar Akpor na jahar Ribas, inda suka halaka yansandan dake gadin baturen, da direbansa, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito yan bindigan sun kai wannan hari ne da nufin sace baturen a yayin da yake cikin ayarin motoci, hakan yasa suka yi ma ayarin motocin kwantan bauna, inda suke bude musu wuta, wanda yayi sanadin mutuwar Yansanda biyu da direba guda daya.

KU KARANTA: Muhimman abinda suka tunzura ni nake neman ɗarewa kujerar shugaban kasa

Bayan yan bindigan sun kashe na kashewa sai suka yi awon gaba da baturen, bugu da kari mutane biyu yan baruwana sun samu munanan rauni a sakamakon ruwan wutan da yan bindigan suka yi akan ayarin motocin, kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Mai kan uwa da wabi: Yan bindiga sun bindige Yansanda biyu, direba a jihar Ribas

Yan bindiga
Source: Depositphotos

Sai dai kaakakin rundunar Yansandan jahar Ribas, DSP Nnamdi Omoni ya tabbatar da mutuwar Yansandan da na direban a wannan hari, sai dai ya musanta batun yin garkuwa da farar fatan.

“Jami’an Yansanda biyu sun gamu da ajalinsu a sanadiyyar harin yan bindiga, yayin mutum daya ke samun sauki sakamakon harbin bindiga daya sameshi, amma babu wani bature ko farar fata da suka sata, kuma rundunar Yansanda ta baza komarta don kama yan bindigan.” Inji DSP Omoni.

A wani labarin kuma jami'an rundunar Yansanda reshen jahar Ogun sun kama wasu manyan limaman Coci guda biyu da laifin kashe wata mata da nufin aikin tsafe tsafe.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel