2019: Nigeria ba ta bukatar tsohon soja ya mulketa: Bafarawa ya canccaki Buhari

2019: Nigeria ba ta bukatar tsohon soja ya mulketa: Bafarawa ya canccaki Buhari

- Alhaji Atahiru Bafarawa ya shawarci yan Nigeria da su kaucewa zabar tsohon soja wanda bai san komai ba sai kashe mutane da kare kansa

- Mai neman takarar shugabancin kasar a zaben 2019, karkashin jam’iyyar PDP ya bayyana cewa idan ya samu nasara zai yiwa kasar garanbawul

- A bangarensa gwamnan jihar Rivers, Wike, ya bukaci yan takarar shugabancin kasar a PDP dasu tabbata sun tunkude APC daga mulki

Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Atahiru Bafarawa ya shawarci ‘yan Nigeria da su guji zabar shugaban kasar da ya taba yin aikin soja, idan aka zo zaben 2019. Acewarsa, tsohon soja ba zai taba zama cikakken dan siyasa ba, kasancewar ba abinda aka horas da shi illla yadda zai kashe mutane da kare kansa.

Bafarawa ya bayyana hakan ne a garin Fatakwal, jihar Rivers, a ziyarar tattaunawa da ya kaiwa shuwagabanni, masu ruwan tsaki, dama mambobin jam’iyyar PDP a jihar.

Ya shaidawa shuwagabannin PDP cewar yana da dukkanin matakan cancantar da ake bukata na shugabantar kasar a wannan karni na demokaradiya.

Nigeria bata bukatar tsohon soja ya mulketa: Bafarawa ya canccaki Buhari

Nigeria bata bukatar tsohon soja ya mulketa: Bafarawa ya canccaki Buhari
Source: Depositphotos

KARANTA WANNAN: Sarkin Kano ya nemi a rika damawa da Almajirai a cikin harkokin boko a Nigeria

Ya ce: “A yau na zo Fatakwal ne don neman goyon bayan jami’an gudanar da zaben fitar da gwani a wannan jam’iyya tamu mai albarka, a zaben fitar da gwani na shugabancin kasar da muke fuskanta. Haka zalika na zo ne don neman shawarwari daga jami’an akan dai batun fitar da gwanin.

“Babban abinda kasar take bukata a yanzu shine ingantaccen tattalin arziki, tsaro da kuma ilimi. Wannan abubuwa sune muhimman abubuwan da zamu maida hankali akansu idan muka samu dama. Zamu yi kokarin ganin yadda zamu fitar da kasarmu daga kunyar data tsinci kanta a ciki yau."

A baya baya dai Bafarawa ya kai ziyarar ta’aziyya ga gwamnan jihar, Nyesom Wike, bisa rasuwar Atoni Janar na jihar, Emma Aguma.

Wike, a lokacin da ya karbi bakuncin Bafarawa, ya yi kira ga daukacin masu neman takarar shugabancin kasar karkashin jam’iyyar PDP za su nemo hanyoyin da zasu tsige gwamnatin APC mai mulki a kasar yanzu.

Sai dai gwamnan ya yi nuni da cewa: “Shi mulki na Allah ne. Idan Allah y ace zakayi to babu makawa sai kayi. Mutane na gwagwarmaya ne kawai, amma ta ubangijine ce dai karshe zata tabbata”

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel