Aisha Buhari tayi alkawarin marawa mata baya a zaben 2019

Aisha Buhari tayi alkawarin marawa mata baya a zaben 2019

Matar Shugaban kasa watau Hajiya Aisha Buhari tayi alkawarin marawa mata da ke takara a 2019 baya. Aisha Buhari tace za ta karfafawa duk mata da su ke neman wata kujerar siyasa a Najeriya baya.

Aisha Buhari tayi alkawarin marawa mata baya a zaben 2019

Matar Shugaban kasa ta sha alwashin goyon-bayan matan da ke siyasa
Source: Depositphotos

Hajiya Aisha Buhari wanda ita ce Uwargidan Shugaban kasa Buhari ta bayyana cewa za ta marawa duk matan da su ka fito takara a zaben 2019 baya. Buhari ta yi wannan jawabi ne ta bakin Mai magana da yawun ta Suleiman Haruna.

Uwargidar Shugaban kasar ta gana da wasu manyan mata ‘Yan siyasa na Yankin Kasar Inyamurai a fadar Shugaban kasa a Ranar Laraba. Uwargidan ta Shugaba Buhari ta nemi mata su tsunduma cikin siyasa domin yi wa kasar su hidima.

KU KARANTA: Bukola Saraki ya shirya tsayawa takarar Shugaban kasa

Matar Shugaban kasar dai tace duk wanda ta tsaya takara a zabe mai zuwa, za ta samu goyon bayan ta. Aisha Buhari tace mata su na cikin wadanda ke zabe don haka yanzu ya kamata su fito takara a Jam’iyyar domin a zabe su a Najeriya.

Buhari ta kuma jinjinawa kokarin da Matan APC ke yi a Kudu maso Gabashin Najeriya ta kuma nemi su kara kwazo. Matar Shugaban kasar tana sa rai mata su kai labari a zaben da za ayi inda ta kuma yi kira a bi dokoki da sharudan Jam’iyya.

Matar Gwammna Imo Mrs. Nkechi Okorocha ce ta jagoranci Matan na Kasar Inyamurai. Sauran wadanda su ka halarci taron sun hada da Shugaban matan APC Salamatu Baiwa, Mrs. Gloria Shoda, Dame Pauline Tallen da Mrs. Juliet Ibekaku.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel