Muhimman abinda suka tunzura ni nake neman ɗarewa kujerar shugaban kasa - Saraki

Muhimman abinda suka tunzura ni nake neman ɗarewa kujerar shugaban kasa - Saraki

A ranar Alhamis, 30 ga watan Agusta ne tsohon gwamnan jahar Kwara kuma shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki ya kaddamar da takararsa na tsayawa zaben shugaban kasar Najeriya.

Sai dai majiyar Legit.ng ta ruwaito Sarakin yana cewa babban burinsa idan har yan Najeriya suka zabe shi a matsayin sabon shugaban kasarsu a zaben shekarar 2019 shine don ya kawo karshe kashe kashe, yunwa, talauci tare da samar da ayyukanyi ga matasa.

KU KARANTA: Jami’an kwana kwana sun ceto wani mutumi yayin da gidan sama ya ruguzo a Kano

A yayin kaddamarwar tasa, Sanata Saraki ya bayyane cewa yana da duk ilimin da kwarewar da ake bukata wajen tafiyar da akalar Najeriya, tare da tsamo Najeriya daga mawuyacin halin da kasar ne ciki.

Muhimman abinda suka tunzura ni nake neman ɗarewa kujerar shugaban kasa

Saraki
Source: Twitter

“Ta ko ta ina a kasar nan, yan Najeriya na kokawa suna neman sauki, yunwa ta damesu, cututtuka nata karkashesu, a yanzu haka akwai yan Najeriya miliyan 87 dake cikin talauci tsundum.

“Wannan matsanancin hali da yan Najeriya ke ciki shine ya haifar da tashe tashen hankula da matsalolin tsaro, idan yunwa da jahilci da kuma rashin madafa suka hadu a kasa, dole ne a fara samun miyagun ayyuka da ayyukan ta’addanci.” Inji Saraki.

Shugaban majalisar ya cigaba da cewa: “Al’ummar kasarnan na cikin tsoro da damuwa sakamakon yawan kashe kashe da sace sacen mutane ga kuma barazanar ta’addanci, duk da haka mun gagara magance matsalolin balle kuma mu shirya ma gaba.

“Duba da dukkanin matsalolin dana zayyano ne tare da duba da kwarewata a sha’anin mulki ne na amsa kiraye kirayen da matasan Najeriya ke yi min, na bayyana burina na tsayawa takarar shugaban kasa don ceto kasar nan.” Inji shi.

Wannan kaddamarwa ta Saraki ya kara yawan adadin yan takarkarun shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar PDP da suka hada da Atiku Abubakar, Sule Lamido, Ibrahim Hassan Dankwambo, Rabiu Kwankwaso, Aminu Waziri Tambuwal, Tanimu Turaki, Ahmed Makarfi da saurans.

Daga cikin wadanda suka halarci bikin kaddamarwar akwai shugaban jam’iyyar PDP, Uche Secondus, da gwamnan jahar Fatakwal kuma jigo a jam’iyyar PDP, Gwamna Nyesom Wike.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel