Ziyarar Theresa May ta ƙarfafa dangartaka tsakanin 'Kasar Birtaniya da Najeriya

Ziyarar Theresa May ta ƙarfafa dangartaka tsakanin 'Kasar Birtaniya da Najeriya

Zaku ji cewa wasu daga cikin 'yan kasuwa na jihar Legas sun bayyana cewa ziyarar Theresa May, firai ministar 'kasar Birtaniya zuwa Najeriya za ta kara bunkasa dangartaka gami da kyakkyawar alaka dake tsakanin kasashen biyu.

Wasu daga cikin mambobin kungiyar 'yan kasuwar na jihar Legas sun bayyana hakan ne bayan ganawar su da Firai Ministar cikin birnin na Legas a ranar Larabar da ta gabata.

Mista Akin Olawore, shugaban kungiyar ta 'yan kasuwa ya bayyana cewa, ganawar ta su da Firai Ministar na da muhimmanci domin inganta dangartarka mai karfin gaske ta habakar tattalin arziki tsakanin kasashen biyu.

Legit.ng ta ruwaito cewa, a ranar Larabar da ta gabata ne Firai Ministar ta Birtaniya ta ziyarci fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda a kan hanyarta ta bankwana ta yada zango a jihar Legas domin tattauna harkokin kasuwanci da masu ruwa da tsaki.

Ziyarar Theresa May ta ƙarfafa dangartaka tsakanin 'Kasar Birtaniya da Najeriya

Ziyarar Theresa May ta ƙarfafa dangartaka tsakanin 'Kasar Birtaniya da Najeriya
Source: Depositphotos

Kazalika, Firai Ministar ta ziyarci kasashen Afirka ta Kudu da kuma Kenya a ranakun Litinin da Talata na wannan mako kafin isowarta Najeriya.

Mista Olaware ya ci gaba da cewa, ana sa ran tattalin arziki na kasuwanci tsakanin kasashen biyu ya habaka zuwa kimanin Fan Miliyan 100 a shekarar nan ta 2018.

KARANTA KUMA: Guguwar sauyin sheƙa ba ta gurgunta jam'iyyar APC ba - Buhari

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, kasar Najeriya ita ce ta biyu a nahiyyar Afirka mafi girman dangantaka da alaka ta kasuwanci tsakanin ta da kasar Birtaniya.

A yayin da wannan shine karo na farko da Firai Ministar ta ziraci nahiyyar Afirka tun hawan ta kujerar mulki a shekarar 2016, Najeriya ta ci gaba da kasancewa kasa mafi fitar da kuma shigo da man fetur da ma'adanan sa daga kasar ta Birtaniya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel