Abubuwa 5 da Bukola Saraki yace zai yi idan ya zama Shugaban kasar Najeriya

Abubuwa 5 da Bukola Saraki yace zai yi idan ya zama Shugaban kasar Najeriya

- Saraki ya kadamar da takarar sa ta shugaban kasa yau

- Yayi wasu muhimman alkawurra da zai cimmawa idan ya zama shugaban kasa

Biyo bayan kaddamar da kudurin takarar sa ta zama shugaban kasar Najeriya da Dakta Bukola Saraki yayi a ranar Alhamis, mun bincika mun kuma zakulo maku abubuwa biyar da yace zai yi idan ya zama shugaban kasar Najeriya.

Abubuwa 5 da Bukola Saraki yace zai yi idan ya zama Shugaban kasar Najeriya

Abubuwa 5 da Bukola Saraki yace zai yi idan ya zama Shugaban kasar Najeriya
Source: Facebook

KU KARANTA: Za'a fara biyan sabon tsarin albashikafin karshen 2018

Idan mai karatu bai manta ba dai kawo yanzu jiga-jigan jam'iyyar ta PDP da dama ne suka bayyana aniyar su ta yin takarar shugaban kasa a zaben 2019 inda kuma suka nuna sha'awar su ta neman tikitin jam'iyyar ta PDP.

Legit.ng ta samu cewa ga dai kadan daga cikin alkawurran da Saraki ya dauka din:

1. Ya sha alwashin fitar da 'yan Najeriya daga cikin kangin talaucin da suke ciki.

2. Ya sha alwashin yin ayyukan more rayuwa a dukkan lungu da sakon kasar nan kamar su hanyoyi da wutar lantarki da ma jirgin kasa.

3. Ya sha alwashin kawo sauye-sauye ga tsarin mulkin kasa ta yadda zai anfani talakawa kai tsaye.

4. Ya sha alwashin samarwa da matasa aikin yi musamman ma kanana da matsakaitan sana'o'i.

5. Ya kuma sha alwashin yin dukkan abun da ya alkawarta yi ba tare da saba alkawari ba ko kuma karairayi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel