Sai fa mun dage indai muna so mu lashe zaben 2019 - Inji Shugaba Buhari

Sai fa mun dage indai muna so mu lashe zaben 2019 - Inji Shugaba Buhari

- Buhari yace sai sun dage sannan su ci zaben 2019

- Ya fadi hakan ne a lokacin taron jiga-jigan APC

- SHugaba Buhari ya jinjinawa shugabannin APC

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya ja hankalin shugabannin jam'iyyar sa ta APC a dukkan matakai da cewa sai fa sun kara zage dantse idan dai har suna so su lashe zabukan da ke tafe na 2019.

Sai fa mun dage indai muna so mu lashe zaben 2019 - Inji Shugaba Buhari

Sai fa mun dage indai muna so mu lashe zaben 2019 - Inji Shugaba Buhari
Source: Facebook

KU KARANTA: Yan luwadi da madigo za su sarara a mulki na inji wani dan takarar shugaban kasa

Shugaban ya yi wannan kalaman ne a lokacin da yake jawabin maraba ga jiga-jigan jam'iyyar ta APC a wajen taron masu ruwa da tsaki na 'yan kwamitin zartarwar jam'iyyar da ya gudana a ranar Alhamis a garin Abuja.

Legit.ng ta samu cewa shugaban ya kuma kara da cewa ya zama wajibi ga shugabannin jam'iyyar su tabbatar da cewa dukkan matsayar da za su dauka ta zama mai anfani ga dukkan 'ya'yan jam'iyyar.

Daga karshe shugaban ya kuma jinjinawa shugabannin jam'iyyar a karkashin jagorancin Kwamared Adams Oshiomhole akan namijin kokarin da sukeyi wajen ganin jam'iyyar ta cigaba da zama tsintsiya madaurin ki daya.

A wani labarin kuma, Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma dan takarar neman tikitin shugaban kasar Najeriyar a karkashin inuwar jam'iyyar PDP a zabe mai zuwa na 2019 watau Atiku Abubakar ya fadi ta cikin sa game da abunda zai yi idan har ya rasa tikitin takarar jam'iyyar.

Fitaccen dan siyasar yace tabbas zai taimaka da dukkan damar da Allah ya bashi don ganin jam'iyyar ta sa tayi nasara koda bai samu tikitin takarar ta ba idan dai har aka yi adalci wajen zaben.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel