Da dumi: Tambuwal ya yanki tikitin takarar kujeran shugaban kasa

Da dumi: Tambuwal ya yanki tikitin takarar kujeran shugaban kasa

- Tambuwal zai yi takara da shugaba Muhammadu Buhari

- Ya siya tikitin zabensa a hedkwatar jam'iyyar PDP

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya yanki tikitin takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Dan siyasan wanda ya sauya sheka daga jam'iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa PDP a farkon watan nan, ya dira hedkwatan jam'iyyar Wadata Plaza a babbar birnin tarayya Abuja da yammacin yau Alhamis, 30 ga watan Agusta, 2018.

KU KARANTA: Sakamakon ganawar kwamitin zantarwan APC; gwamnoni sun samu galaba

Ya isa hedkwatan misalin karfe 6 na yamma.

‎Ya bayyanawa manema labarai cewa yanada tabbacin cewa shugabannin jam'iyyar zasu gudanar da zaben fidda gwani da gaskiya idan ba'a zabi mutum daya kafin zabe ba.

Yace: "Ba zan iya cewa babu bukatar zaban mutum daya ba; hakan na cikin demkoradiyya. Idan akwai yiwuwan haka, a yi, amma idan hakan bai samu ba, zamu hadu a zaben fidda gwani,".

"Amma inada imanin cewa PDP a yau za ta iya shirya zaben fidda gwani cikin zaman lafiya da lumana."

"Na san idan kuka duba siyasata a baya. Na dade ina fuskantar kalubale yan adawa haka. Ku tua yadda na zama kakakin majalisar wakilai da kuma yadda na cigaba da kasancewa kakakin."

"Saboda haka hankali bai tashi akan duk abinda zai taso a matsayin kalubale daga gwamnati."

Tambuwal ya zama kakakin majalisar wakilai a shekarar 2011 zuwa 2015. Daga nan ya zama gwamnan jihar Sokoto.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel