Atiku Abubakar ya fadi abunda zai yi idan ya rasa tikitin takara a PDP

Atiku Abubakar ya fadi abunda zai yi idan ya rasa tikitin takara a PDP

- Atiku yace zai yi iya kokarin sa wajen ganin PDP ta kada Buhari

- Amma yace sai in anyi adalci a cikin zaben fitar da gwani

- Yace kuma ba zai sake fita daga PDP ba

Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma dan takarar neman tikitin shugaban kasar Najeriyar a karkashin inuwar jam'iyyar PDP a zabe mai zuwa na 2019 watau Atiku Abubakar ya fadi ta cikin sa game da abunda zai yi idan har ya rasa tikitin takarar jam'iyyar.

Atiku Abubakar ya fadi abunda zai yi idan ya rasa tikitin takara a PDP

Atiku Abubakar ya fadi abunda zai yi idan ya rasa tikitin takara a PDP
Source: Twitter

KU KARANTA: Wani babban malamin izala ya ci kudin masallaci a Kano

Fitaccen dan siyasar yace tabbas zai taimaka da dukkan damar da Allah ya bashi don ganin jam'iyyar ta sa tayi nasara koda bai samu tikitin takarar ta ba idan dai har aka yi adalci wajen zaben.

Legit.ng ta samu cewa Atiku ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da wasu jiga-jigan jam'iyyar ta PDP na jihar Neja a garin Minna babbar birnin jihar a cigaba da ziyarar neman goyon baya da yake kai wa jahohi.

Haka zalika tsohon shugaban ya kuma ce yana da yakinin cewa shine zai lashe zaben fitar da gwanin jam'iyyar sannan kuma ya sake jaddada alkawarin da ya dauka na cewa ba zai kara fita daga jam'iyyar sa ta PDP ba.

A wani labarin kuma, Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya ja hankalin shugabannin jam'iyyar sa ta APC a dukkan matakai da cewa sai fa sun kara zage dantse idan dai har suna so su lashe zabukan da ke tafe na 2019.

Shugaban ya yi wannan kalaman ne a lokacin da yake jawabin maraba ga jiga-jigan jam'iyyar ta APC a wajen taron masu ruwa da tsaki na 'yan kwamitin zartarwar jam'iyyar da ya gudana a ranar Alhamis a garin Abuja.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel