Shugaban UN ya yabi tsohon Shugaban kasar Najeriya Obasanjo

Shugaban UN ya yabi tsohon Shugaban kasar Najeriya Obasanjo

Labari ya zo mana cewa Majalisar Dinkin Duniya UN ta yabawa kokarin da tsohon Shugaban Kasar Najeriya Cif Olusegun Obasanjo a wajen kokarin da yayi a Kasar Liberiya ta Afrika a 2017 lokacin da aka samu canjin Gwamnati a kasar.

Shugaban UN ya yabi tsohon Shugaban kasar Najeriya Obasanjo

Obasanjo yana cikin wadanda su ka kawo juyin Gwamnati a Liberiya
Source: Getty Images

Shugaban Majalisar Dinkin Duniyar Antonio Guterres ya yabi tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ne game da irin kokarin da yayi wajen ganin an samu zaman lafiya a Kasar Liberiya a wajen wani taro da aka yi a Kasar Amurka.

Antonio Guterres yayi jawabi ne wajen wani taro da aka shirya na kasashen Duniya a babban Hedikwatar Majalisar Dinkin Duniyar da ke cikin Garin New York. Guterres yace Obasanjo yana cikin wadanda su kayi wa UN hidima.

KU KARANTA: APC ta kawo sabon tsarin fitar da 'Dan takara a 2019

Majalisar ta UN tace Obasanjo yana cikin manyan da aka aika zuwa Kasar Liberiya domin ganin an canji mulki a Kasar. Shugaban na UN yace Obasanjo ne ya wakilce sa lokacin a Kasar Liberiya inda yayi amfani da damar ya gode masa.

Tsohon Shugaban na Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya taba sa-baki wajen ganin an samu zaman lafiya a kasashen Afrika irin su Angola, Burundi, Mozambik, da Nambiya da kuma Kasar Afrika ta Kudu da kuma irin su Kasar Sierra Leone.

Shugaban na UN Guterres yace irin su Obasanjo su na cikin manyan da ya ke daukar shawarar su a Duniya. Bayan nan kuma Shugaban na UN yace Obasanjo yana cikin wadanda su ke zama madubin dubawa ga yara ‘yan bana-bakwai.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel