2019: Abubuwa 8 da Saraki ya fada yayin kaddamar da takararsa ta shugaban kasa

2019: Abubuwa 8 da Saraki ya fada yayin kaddamar da takararsa ta shugaban kasa

A yau, Alhamis, ne shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, ya bayyana sha’awarsa ta yin takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP

Saraki ya zayyana wasu abubuwa har guda 8 da suka saka shi yanke shawarar shiga takarar shugaban kasar Najeriya

Yawan masu neman jam’iyyar PDP ta tsayar da su takarar shugaban kasa ya karu ya zuwa mutane 12, dukkan su daga arewacin Najeriya.

Tun bayan ficewarsa daga APC ake hasashen cewar Saraki ya fita daga jam’iyyar ne domin yana son yin takarar shugaba, ita kuma APC din ta yanke shawarar kara bayar da tikintinta ga shugaba Buhari.

2019: Abubuwa 8 da Saraki ya fada yayin kaddamar da takararsa ta shugaban kasa

2019: Abubuwa 8 da Saraki ya fada yayin kaddamar da takararsa ta shugaban kasa
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: A karo na farko bayan tsige shi, Lawal Daura ya yi magana kan mamaye majalisa

A yayin kaddamar da takarar sa, Saraki ya zayyana wasu abubuwa da suka saka shi yin takarar tare da abubuwan da zai yi idan aka zabe shi kamar haka:

1. Mutanen Najeriya nma neman mai ceton su daga kangin fatara da yunwa da suka samu kansu a ciki. ‘Yan Najeriya na rayuwa kasa da mizanin talauci duk da arzikin da kasar ked a shi.

2. Tattalin arzikin Najeriya ya karye, yana bukatar a farfado das hi cikin gaggawa. Tabarbarewar tattalin arziki ta jawo asarar aiyuka tare da durkushewar kasuwanci.

3. Ina son ganin matasa na taka muhimmiyar rawa a al’amuran gwamnatin Najeriya da ma harkokin kasuwanci da sana’o’i.

4. Zan bawa matasa dukkan dammar da suke bukata domin ganin sun zama masu ruwa da tsaki a harkokin gudanar da gwamnati a Najeriya.

5. Jama’ar Najeriya na bukatar shugabanci da zasu yi alfahari da shi, shugabancin da nahiyar Afrika da Duniya baki daya zata so.

6. Zan kare hakki da mutuncin ‘yan Najeriya da kundin tsarin mulki. Zan yi aiki da doka kamar yadda yake shimfide cikin tsarin siyasa.

7. Zan tsare rayuka da dukiyar ‘yan Najeriya ta hanyar sake fasalin tsaron kasa tare da samar da isassun kayan aiki ga jami’an tsaron mu.

8. Da wannan nake sanar da ‘yan Najeriya burina na son yin takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP a zaben shekarar 2019 mai zuwa domin kafa gwamnati ta jama’a da zata yi tafiya da kowa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel