Ficewar Saraki karfi ta karawa APC - Oshiomhole

Ficewar Saraki karfi ta karawa APC - Oshiomhole

- Kowacce jam'iyyar siyasa na son karin mambobi amma shugaban APC na kasa ya ce da shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki a sauka lafiya bayan ficewarsa

- Shugaban majalisar dai ya fice daga APC ne sakamakon korafin yaga musu rigar arziki da ake yi

Jim kadan bayan bayyana ra'ayin Bukola Saraki na son tsayawa takarar shugabancin kasar nan, Shugabancin jam'iyyar APC ya bayyana cewa jam'iyyar tafi zama daidai bayan ficewar tasa.

Da yake ganawa da manema labarai jim kadan bayan fitowarsa daga taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar ta APC, Shugaban jam'iyyar Adams Oshiomhole, ya bayyana cewa jam'iyyar tafi tafiya daidai bayan da Saraki da sauran wadanda suka sauya shekar suka fice.

Ficewar Saraki karfi ta karawa APC - Oshiomhole

Ficewar Saraki karfi ta karawa APC - Oshiomhole
Source: Depositphotos

Oshiomhole ya ce "Jam'iyyarmu tafi tafiya da zama daidai bayan da suka fice, kuma za’a iya ganin hakan saboda musamman a zabukan da muka gudanar".

"A lokacin da suke jam'iyyar nan ba wanda ya hana su damar bayyana ra'ayinsu, amma da yake kasuwar bukatarsu ce a gaba shi yasa suka sauya sheka".

KU KARANTA: Ba bu hannun mu cikin 'dambarwar taron Kwankwaso a garin Abuja - APC

Shugaban jam'iyyar ya kara da cewa duk wanda suke sauya shekar basu da wata alkibibla a siyasa face sauya gida daga wani zuwa wani".

Har wa yau, ya ce duk wani dan siyasar da yake irin wannan ba komai bane face dan gudun hijirar siyasa.

Adam Oshiomhole ya kuma yi amfani da wannan dama wajen godewa shuwagan kasa Muhammadu Buhari sakamakon yarda da shugabanci da kuma 'ya'yan jam'iyyar ta APC.

Ficewar Saraki karfi ta karawa APC - Oshiomhole

Ficewar Saraki karfi ta karawa APC - Oshiomhole
Source: Depositphotos

"Abin alfahari ne a lokacin da muka fara shugabancin jam'iyyar nan, mun samu nasarori kama daga matakin jihohi har zuwa tarayyar kasar nan. Tabbas shugaban kasa ka bada gudunmawa gaya wajen samun wannan nasoriri." Oshiomhole ya bayyana.

Saraki dai ya kaddamar da bukatarsa ta son takarar shugabancin kasar nan karkashin inuwar jam'iyyar PDP a yau, bayan da ya biyo bayan mutane da dama dake zawarcin wannan tikitin takara na shugabancin kasar nan.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel