Yadda barazana ta sa yan jarida yin zanga zanga a jihar Abia

Yadda barazana ta sa yan jarida yin zanga zanga a jihar Abia

- Yan jarida a jihar Abia sun gudanar da zanga zangar lumana kan irin hare-haren da ake kai masu a yayin gudanar da ayyukansu

- Shugaban kungiyar NUJ a jihar ya ce kashe kashen 'yan jarida da rushe gidajen watsa labarai ya fara zama abin tsoro

- Wannan zanga zangar umurni ne daga uwar kungiyar 'yan jarida ta kasa NUJ.

A ranar Alhamis 30 ga watan Augusta, dandazon 'yan jarida a jihar Abia suka shiga sahun takwarorinsu na sauran kasashen duniya, wajen gudanar da zanga zangar Allah-wadai da irin hare haren da ake kawai yan jarida da kuma hantar aikin.

Wannan zanga zangar umurni ne daga uwar kungiyar 'yan jarida ta kasa NUJ.

Yan jaridar sun yi zanga zangar ne ta hanyar kewaye sakatariyar kungiyar dake lamba 1, titin Aba, da kuma kewaye babban ginin Umuahia, kusa da ofishin karba da aika sako da ke a babban birnin jihar.

KARANTA WANNAN: Sabon bincike: Awaki na iya banbance mutane masu fushi da masu fara'a

Masu zanga zangar na dauke da kwalaye da aka yi rubutu a jiki, kamar su: "Kashe aikin jarida tamkar kashe demokaradiya ne", "Tura fa ta kai bango, aikin jarida ba zunubi bane" da kuma "Muna Allah-wadai da cin fuskar da akeyiwa aikin jarida", da dai sauransu.

A takaitaccen jawabinsa, shugaban kungiyar na jihar, John Emejor, ya buga misalai da irin yadda aka kashe wasu 'yan jarida, ko hantararsu, uwa uba ma yadda jami'an tsaro suka rinka dukansu.

Ya ambaci rushe gidan rediyon Fresh FM (Music House) a Ibadan, jihar Oyo, wanda gwamnatin jihar tayi, yana mai cewa ire iren wadannan hare-haren barazane ga rayukan yan jarida a kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel