Abin da zan yi idan na samu mulkin Shugaban kasa a 2019 - Kwankwaso

Abin da zan yi idan na samu mulkin Shugaban kasa a 2019 - Kwankwaso

Mun ji cewa tsohon Gwamnan Jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso yayi alkawarin gyara Najeriya idan har ya samu mulkin Kasar nan a karkashin Jam’iyyar adawan PDP a zabe mai zuwa na 2019.

Abin da zan yi idan na samu mulkin Shugaban kasa a 2019 - Kwankwaso

Sanata Kwankwaso yayi alkawarin gyara Najeriya
Source: Depositphotos

Tsohon Gwamna Sanata Rabiu Kwankwaso yayin da yake jawabi wajen kaddamar da shirin sa na tsayawa takarar Shugaban kasa jiya a babban Birnin Tarayya Abuja yayi alkawain kawo zaman lafiya a fadin Najeriya idan ya zama Shugaba.

Kwankwaso yayi alkawarin yi wa kasar nan garambawul ta fuskar tattalin arziki da kuma siyasa da walwalar jama’a. Tsohon Gwamnan yace Gwamnatin sa za ta hada-kan ‘Yan Najeriya tare da bunkasa harkar tattalin arziki idan ya hau mulki.

KU KARANTA: PDP ta bayyan karyar da APC ta yi wa Najeriya a 2015

Rabiu Kwankwaso wanda yayi Ministan tsaro a lokacin Gwamnatin Obasanjo ya bayyana cewa zai kawo karshen rikicin Boko Haram da ta’adin Makiyaya da Masu garkuwa da mutane idan har ya zama Shugaban kasar Najeriya a 2019.

Sanatan na Kano ta tsakiya yayi alkawarin ganin masu rike da madafan iko sun daina amfani da Jami’an tsaro wajen cin ma burin siyasa. Sanata Kwankwaso yace zai dage wajen ganin ‘Yan Sanda da Sojoji sun kara karfi a Najeriya.

Tsohon Gwamnan na Kano ya koka da halin da Najeriya ta shiga a Gwamnatin Buhari musamman ta fuskar tattalin arziki. ‘Dan takarar Shugaban kasan a Jam’iyyar PDP ya kuma sha alwashin inganta harkar ilmi idan yayi nasara a 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel