APC ba za ta yi kewar yan siyasa masu juyi kamar dutse ba – Oshiomhole

APC ba za ta yi kewar yan siyasa masu juyi kamar dutse ba – Oshiomhole

- Adams Oshiomhole ya caccaki yan siyasar dake sauye-sauyen sheka

- Yace APC ba za ta yi kewar yan siyasar da suka mayar da sauya sheka al'adarsu ba

- Shugaban na APC ya bayyana su a matsayin yan gudun hijira da kuma dutse mai juyi

Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Adams Oshiomhole ya bayyana cewa jam’iyyar ba za ta yi kewar ‘yan siyasar da suka mayar da sauya sheka daga jam’iyya guda zuwa wata halinsu a duk lokacin da zabe ya gabato.

Da yake bayyana su a matsayin yan siyasar gudun hijira da dutse mai juyi, shugaban jam’iyyar ya bayyana hakan a wajen taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar wanda aka gudanar a sakatariyar jam’iyyar na kasa dake Abuja.

A cewarsa a lokacin da ya karbi shugabancin jam’iyyar, ya yi yunkurin kawo zaman lafiya a tsakanin wadanda ke fafutuka da zuciya daya wanda yake ganin jam’iyyar zata iya magancewa.

APC ba za ta yi kewar yan siyasa masu juyi kamar dutse ba – Oshiomhole

APC ba za ta yi kewar yan siyasa masu juyi kamar dutse ba – Oshiomhole
Source: Facebook

Amma wadanda suka barsu suna ganin ba zasu iya cimma kudirinsu a karkashin jam’iyyar ba.

A baya Legit.ng ta tattaro cewa wata kungiyar siyasa mai kokarin ganin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu nasarar zarcewa a zaben 2019 mai suna Good Governance Ambassadors of Nigeria (GOGAN) tayi kira ga mutanen yankin kudu maso gabas da su marawa shugaban kasar baya domin ya samar masu hanya da mutumin Igbo zai zamo shugaban kasa a 2023.

KU KARANTA KUMA: Rabuwar kai a jam’iyyar APC kan tsarin gudanar da zaben fidda gwani yayinda kwamitin zantarwa za ta gana yau

Shugaban kungiyar na kasa, Cif Felix Idiga wanda yayi wannan kira a lokacin ganawar kungiyar a Abuja, ya bukaci yan Igbo da kada su bari wannan dama ya kubuce masu na ganin yankin su sun wadanda zasu gaji Shugaba Buhari.

Cif Idiga yayi gargadin cewa yankin kudu maso gabas na iya rasa wata dama har sai shekaru ashiri masu zuwa idan har basu yi amfani da damarsu da hikima ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel