Mun gaji da bakin ikon da Saraki ke nuna mana - Mutanen jihar Kwara

Mun gaji da bakin ikon da Saraki ke nuna mana - Mutanen jihar Kwara

Al-ummar mazabar Ajikobi da karamar hukumar Ilorin ta yamma na jihar Kwara sun ce sun gaji da bakin ikon da Saraki da iyalansa ke nuna musu hakan yasa suka yanke shawarar raba jiha da shi da duk wani da ya tsayar.

Wani shugaban al'umma kuma jigo a jam'iyyar APC a Ajikobi, Omar Aiyelabegan, wanda ya yi magana da manema labarai a gidansa da ke Ilorin a ranar Juma'a, ya ce babu wanda sai amince da irin kama-karyar da Saraki ke musu a jihar.

"Muna da ra'ayin kanmu, ko yara na suna da ikon su zabi jam'iyyar da za ta amfane su, mun gaji da Bukola Saraki, inji shi.

Mun gaji da bakin ikon da Saraki ke nuna mana - Mutanen jihar Kwara

Mun gaji da bakin ikon da Saraki ke nuna mana - Mutanen jihar Kwara
Source: Depositphotos

Mr Aiyelabegan ya ce dama tun farko jama'ar Kwara basu amince Saraki ya zama shugabansu ba.

DUBA WANNAN: Yadda muka shawo kan Jonathan ya amince da sakamakon zaben 2015 - Janar Abdulsalami

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ta ruwaito cewa mazabar Ajikobi ce mazabar shugaban majalisa, Bukola Saraki, kuma gidan Aiyelabegan yana kusa da gidan iyayen Bukola Saraki.

Mr Aiyelabegan ya koka cewa iyalan Saraki musamman shugaban majalisar dattawan bai kawo wasu ababen cigaba ko more rayuwa a yankin Agbaji da kewaye.

"Sai lokacin zabe ta karato ne kawai za su kusanci talakawa su lasa musu alewa a baki saboda su jefa musu kuri'a," inji Aiyelabegan.

Kazalika, Mr Aiyelabegan ya gargadi shugaba Muhammadu Buhari ya yi taka tsan-tsan da masu yiwa Saraki biyaya a jihar da kasa da ke ikirarin har yanzu su 'yan jam'iyyar APC ne.

A cewarsa, mutanen Kwara sun bayyana Saraki cewa zamaninsa ya wuce hakan yasa Saraki ya fadi zabe har a akwatin zaben da ke garinsu ta Agbaji.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel