Da dumi-dumi: Sakamakon ganawar kwamitin zantarwan APC; gwamnoni sun samu galaba

Da dumi-dumi: Sakamakon ganawar kwamitin zantarwan APC; gwamnoni sun samu galaba

- An raba gardama tsakanin yan jam'iyyar APC kan zaben fidda gwani

- Daga karshe an sabawa ra'ayin shugaban jam'iyyar Adams Oshiomole

Bayan dogon tattaunawa da muhawara, jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta yanke shawaran amfani da tsarin kullaliyar zaben fidda gwani a dukkanin kujerun takara sabanin kujeran shugaban kasa.

An yanke wannan shawara ne a taron ganawar masu ruwa da tsaki a jam'iyyar da akayi a yau Alhamis, 30 ga watan Agusta, 2018 a sakatariyan jam'iyyar ta kasa da ke Abuja.

Gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong, ya bayyanawa manema labarai cewa jihohi zasu iya zaben buddadiyar zaben fidda gwani idan bukatan haka ya zo.

KU KARANTA: Buhari, Osinbajo, Tinubu sun hallara a ganawar kwamitin zantarwan APC

Menene kullaliyar zaben fidda gwani?

"Abinda ake nufi da kullaliyar zaben fidda gwamni shine zaben da wasu zababbun deleget zasu zabi wanda zai wakilci jam'iyyar a takaran ko wani kujera."

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa An samu gagarumin rabuwar kai a jam’iyya mai mulki ta All Progressives Party (APC) kan sabuwar tsarin gudanar da zaben fidda gwani da jam’iyyar ke shirin amfani da shi gabanin zaben 2019.

Majiya a jamiyyar sun bayyanawa jaridar Daily Trust cewa a jiya, yawancin yan jam’iyyar musamman gwamnoni sun nuna rashin yardarsu da bari mambobin jam’iyya gaba daya su kada kuri’a wajen zaben fidda gwani.

Wannan tsari ya fi kwantawa babban jigon jam’iyyar, Bola Tinubu, da shugaban jam’iyyar, Adams Oshiomole.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel