'Yan sanda sunyi ram da wani tsohon da ya haikewa ‘yar makwabtansu mai shekara 11

'Yan sanda sunyi ram da wani tsohon da ya haikewa ‘yar makwabtansu mai shekara 11

- Jami'an tsaro sun cafke wani dattijon da ya yiwa karamar yarinya fyade

- Sai dai ya kyankyasa kasa ya ce bai aikata ba, kafin daga bisani ya sha matsa ya amsa laifinsa

Jami'an rundunar ‘yan sandan jihar Legas sun kama wani mutum mai suna Felix Idehen dan kimanin shekaru 54 bisa zarginsa da yiwa wata yarinya mai kimanin shekaru 11.

An dai bayyana cewa mutumin da ake zargin yayi aika-aikar makwabcin iyayen yarinyar ne, mazauna unguwar Shomolu. inda ya yi amfani da damar makwaftakar wajen aiwatar da mugun nufinsa.

'Yan sanda sunyi ram da wani tsohon da ya haikewa ‘yar makwabtansu mai shekara 2 kacal

'Yan sanda sunyi ram da wani tsohon da ya haikewa ‘yar makwabtansu mai shekara 2 kacal
Source: Facebook

Tun da farko dai wasu rahotanni sun bayyana cewa Felix yana sana'ar tuki ne, kuma ya fara yiwa yarinyar fyade ne tun a Shekarara ta 2016, amma sai dai dubunsa ta cika ne a shekarar da muke ciki ta 2018.

KU KARANTA: Abinda ya sa Obasanjo ke son in zama shugaban kasa - Lamido

Wata kungiya mai yaki da yiwa yara fyade ce ta gabatar da korafin ga ofishin ‘yan sanda na Onipanu, ta bakin shugaban kungiyar Toying Okanlawon.

Bayan gabatar da korafin ne, sai jami'an ‘yan sandan suka damke Felix, sai dai ya musanta zargin da ake masa, amma daga baya ya amsa aikata laifin yayin da ya sha tuhuma.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel