Yanzu Yanzu: Saraki ya kaddamar da kudirinsa na takarar shugaban kasa

Yanzu Yanzu: Saraki ya kaddamar da kudirinsa na takarar shugaban kasa

- Bukola Saraki ya bayyana aniyarsa na takarar kujerar shugaban kasa a zabe mai zuwa

- Yace zai yi taakarar ne akarkashin lemar jam'iyyar PDP

- Shugaban majalisar dattawan ya sha alwashin kawo ci gaban Najeriya da yan Najeriya

Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya bayyana kudirinsa na takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2019.

Ya kaddamar da kudirin nasa ne a ranar Alhamis, 30 ga watan Agusta yayinda yake zantawa da matasa masu neman takara a babban birnin tarayya, Abuja.

An tattaro inda Saraki ke cewa: “Don haka ina sanar da kudirina na takarar kujerar shugaban kasar tarayyar Najeriya a zabe mai zuwa a 2019 a karkashin jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP).

“Nayi hakan ne tare da yakinin cewa ina da abunda ake bukata wajen kawo ci gaban Najeriya da yan Najeriya.”

Ga bidiyon dake dauke da cikakken bayanansa a kasa:

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Kungiyar matasan Arewa mai suna Northern Youths for Peace and Security (NYPS), a jiya Laraba, 29 ga watan Agusta sun tsayar da shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki a matsayin zabinsu na takarar kujerar shugaban kasa a zabe mai zuwa.

KU KARANTA KUMA: Hadimin Dogara ya shiga takarar kujerar dan majalisa na jiha a karkashin PDP

Shugaban kungiyar, Salisu Magaji, ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Jalingo, babban birnin jihar Taraba, bayan wani ganawa tare da manyan matasan arewa.

Magaji ya bayyana cewa shawarar da kungiyar ta yanke ya kasance akan yadda da tayi da cewa gwamnati mai ci ta gaza sosai sannan kuma cewa Saraki ne mutum da ake ganin yana da abunda ake bukata don ceto Najeriya daga halin da take ciki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel