Wasu manyan limaman Coci sun shiga hannu bayan sun kashe wata mata

Wasu manyan limaman Coci sun shiga hannu bayan sun kashe wata mata

Ni y’asu, mun shigo wani zamani da tausayi yayi karanci a tsakanin jama’a, gogoriyon neman abin duniya shi jama’a suka sanya a gaba, amana ta yi wuya, mutum bai ma san wanda zai yarda shi ba, a yanzu ba karamin abu bane gane mutumin kirki da na tsiya, wannan shine halin da muka tsinci kanmu a ciki.

Anan jami’an rundunar Yansandan jihar Ogun ne suka tsinkayi gidan wani babban limamin Coci, inda suka samu nasarar kama shi da wani abokin aikinsa sakamakon zargin aikata laifinsa kisan kai dake rataye a wuyansu, inji rahoton gidan talabijin na Channels.

KU KARANTA: Bafarawa ya yi watsi da duk wani tayin sulhu da sauran yan takarar shugaban kasa

Majiyar Legit.ng ta ruwaito fastocin da aka kama sun hada da Ayodele Bamiduro da Olushola Akindele, wanda ake zarginsu da kashe wata mata a unguwatr Ijoko na jahar Ogun, inji kwamishinan Yansandan jahar, Ahmed Iliyasu.

Kwamishina Ahmed yace sun samu nasarar kama Fastocin ne bayan samun korafi daga hakimin yankin karamar hukumar Ifo, wanda ya shaida ma yansanda cewa sun gano gawar wata mata daya fara rubewa a cikin wani kango.

“Wannan gawar bata rasa nasaba da ayyukan kungiyoyin matsafa” inji Ahmed, sa’annan yace zasu gurfanar da wadanda ake zargi gaban kotu da zarar sun kammala gudanar da bincike.

Daga karshe kwamishinan ya tabbatar ma jama’an yankin cewa rundunar Yansanda zata yi iya bakin kokarinta don ganin ta kawo karshe makamancin ayyukan nan a tsakanin al’umma, tare da tabbatar da an hukunta duk masu aikata miyagun laifuka.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel