Sauya Fasali: Jam'iyyar PDP ta zargi APC da yiwa 'yan Najeriya 'karya

Sauya Fasali: Jam'iyyar PDP ta zargi APC da yiwa 'yan Najeriya 'karya

Jam'iyyar PDP ta caccaki lafuza gami da sukar kalaman mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, da ya bayyana cewa sauya fasalin kasar nan ba ya daya daga cikin kalubalen da Najeriya take fuskanta a halin yanzu.

Mataimakin shugaban kasar yayin zaman sauraron ra'ayin al'ummar Najeriya a birnin Minneapolis na kasar Amurka ya bayyana cewa, a halin yanzu Najeriya ba ta bukatar sauyin fasali wanda hakan ya sabawa alkawari na gwamnatin su ta jam'iyyar APC.

A sanadiyar haka jam'iyyar adawa ta PDP ke kausasa harshe dangane da wannan furuci na Osinbajo, wanda ya sabawa kudirin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauka yayin yakinsa na neman zabe a shekarar 2015.

Jam'iyyar PDP take cewa, kalaman Osinbajo sun kara tabbatar da cewa jam'iyya mai ci ta APC ta shirga karya ne kurum ga al'ummar Najeriya domin yaudarar su ta samun nasara a zaben 2015.

Sauya Fasali: Jam'iyyar PDP ta zargi APC da yiwa 'yan Najeriya 'karya

Sauya Fasali: Jam'iyyar PDP ta zargi APC da yiwa 'yan Najeriya 'karya
Source: Depositphotos

PDP ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da sanadin kakakin ta, Mista Kola Ologbondiyan, yayin ganawar sa da manema labarai cikin babban birnin kasar nan na tarayya a ranar Larabar da ta gabata.

KARANTA KUMA: Ina nan daram a jam'iyyar PDP ko da na rasa Tikitin takara - Sule Lamido

Mista Kola ya shaidawa manema labarai cewa, kudirin sauya fasalin da tsare-tsaren kasa na daya daga cikin muhimman akidu na jam'iyyar APC wanda a halin yanzu ya shiga sahun alkawurra na shagulatan bangaro da ta gaza cikawa.

A sanadiyar haka kakakin jam'iyyar yake kira ga al'ummar kasar nan akan su dauki izina gami da shiga taitayin su kan duk wani alkawari da jam'iyyar ta APC za ta yi a yayin da babban zabe na 2019 ke ci gaba da karatowa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit

Mailfire view pixel