NIS ta bukaci masu bukatar fasfot da suyi amfani da shafinta na yanar gizo

NIS ta bukaci masu bukatar fasfot da suyi amfani da shafinta na yanar gizo

- Hukumar NIS ta bukaci masu son mallakar Fasfo, da su cike bayanansu da biyan kudi kai tsaye ta hanyar shafin hukumar na yanar gizo

- Wannan mataki ya biyo bayan mutuwar wani mutumi a lokacin da yake zaman jiran karbar takardarsa a wani ofishin hukumar a jihar Legas

- Hukumar ta ce cike bayanan bukatar samun fasfot ta yanar gizo zai saukakawa hukumar dama jama’a baki daya

Hukumar shige da fice ta kasa (NIS) ta bukaci masu son cike bukatar samun takardar fasfot, da su yi amfani da shafin hukumar na yanar gizo. Haka zalika ta bukace su da suyi amfani da shafin wajen biyan kudaden su, don rage wahalhalu da dogon lokacin da ake batawa wajen samar da takardun.

Wannan mataki ya biyo bayan mutuwar wani mutumi, da ke kokarin samun sabon fasfot a ofishin hukumar ta NIS da ke Ikoyi, jihar Legas.

Da yake jawabi dangane da irin matsalolin da masu cike takardun ke samu a ofisoshin hukumar da ke a fadin kasar, Amos Okpu, wanda yayi magana a madadin hukumar ta NIS, ya ce: “Masu cike takardun ne ke wahalar da kawunansu.”

KARANTA WANNAN: Hukumar INEC tasha alwashin gurfanar da duk wanda ta samu da laifin siyen kuri'u

“Dalilina na cewa haka kuwa shine, gwamnati ta samar da shafinta na yanar gizo da za’a iya cike bayanan bukatar samun fasfo dama biyan kudaden kai tsaye ta shafin, duk don saukakawa jama’a, amma da yawan mutane sun zabi zuwa ofishoshinmu, wanda hakan ke sa kowa ya jigata”

Ya bayyana cewa da yawa da ga cikin ofishoshin hukumar NIS na gaza daukar mutanen da ke zarya cikinsu kullum, hakan ke sawa masu cike takardun ke fuskantar rashin gamsuwa, yayin zaman jiran karbar takardar.

Okpu, don haka ya bukaci duk wadanda ke son mallakar Fasfot, da ya cike duk bayanan da ake bukata da kuma biyan kudinsa ta shafin hukumar na yanar gizo, don saukakawa da kuma rage yawan dogon lokacin da ake dauka don samar da takardar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel