Attajirai 15 za su dauki nauyin Takarar Bianca Ojukwu

Attajirai 15 za su dauki nauyin Takarar Bianca Ojukwu

Da sanadin shafin jaridar The Punch mun samu rahoton cewa, akwai kimanin attajirai 15 da za su dauki nauyin takarar kujerar Sanata ta Bianca Ojukwu, uwargidan tsohon shugaban kabilar Ibo, Marigayi Dim Chukwuemeka Ojukwu.

Tsohon gwamnan jihar Imo, Cif Ikedi Ohakim, shine ya bayyana hakan da cewar 'yan kabilar ba za su zuba idanu wani ya kawo wargi ga mai dakin tsohon shugaban su a yayin cimma kudirin ta na neman kujerar Sanatan jihar Anambra ta Kudu.

Ohaki wanda ya musalta Marigayi Ojukwu a matsayin adalin jagora raye ko a mace, ya bayyana hakan ne yayin taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APGA da aka gudanar a karamar hukumar Aguata ta jihar Anambra.

Ya umurci wadanda ke son yin takara tare da Bianca akan su sauya tunani tare da jaddada cewa, hakan zai janyo koma baya ga kasar Inyamurai a sanadiyar adawa da Marigayi Ojukwu dangane da takara da Uwargidan sa da dukkanin dangin sa baki daya.

Attajirai 15 za su dauki nauyin Takarar Bianca Ojukwu

Attajirai 15 za su dauki nauyin Takarar Bianca Ojukwu
Source: Facebook

Duk da cewa manema takarar na da tarin dukiya ta fafata takara da uwargidan Marigayi Ojukwu, sai dai ba bu wanda ke da martaba da kuma nasaba makamanciyarta kamar yadda tsohon gwamnan ya bayyana.

KARANTA KUMA: Ba bu hannun mu cikin 'dambarwar taron Kwankwaso a garin Abuja - APC

Ya ci gaba da cewa, an tanadi kimanin hamshakan attajirai 15 da kuma fiye da matasa 25, 000 da sadaukar da kawunan su domin cimma nasarar kujerar Sanata ga Bianca, inda yake kira ga al'ummar jihar Anambra akan kada su kunya Bianca kan wannan kudiri da sanya a gaba.

Legit.ng ta ruwaito cewa, Bianca wadda tsohuwar jakadan Najeriya ce zuwa kasar Andalus, ta na neman takarar kujerar Sanatan jihar Anambra ta Kudu karkashin inuwa ta jam'iyyar APGA wadda Marigayi Mai gidanta ya jaddada kafuwarta gami da jagoranci na fiye da tsawon shekaru goma a yayin rayuwar sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel