Yanzu-yanzu: Buhari, Osinbajo, Tinubu sun hallara a ganawar kwamitin zantarwan APC mai muhimmanci

Yanzu-yanzu: Buhari, Osinbajo, Tinubu sun hallara a ganawar kwamitin zantarwan APC mai muhimmanci

Shugaba Muhammadu Buhari da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo da wasu mambobin kwamitin zantarwan jam’iyya ami mulki ta All Progressives Congress sun hallara a sakatariyan jam’iyyar ta kasa dake birnin tarayya Abuja.

Shugaba Buhari ya isa sakatariyan misalin karfe 11:19 na safen an kafin sauran masu ruwa da tsaki a jam’iyyar suka iso.

Daga cikin wadanda sukayi saurin zuwa sune babban jigon jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Yanzu-yanzu: Buhari, Osinbajo, Tinubu sun hallara a ganawar kwamitin zantarwan APC mai muhimmanci

Yanzu-yanzu: Buhari, Osinbajo, Tinubu sun hallara a ganawar kwamitin zantarwan APC mai muhimmanci
Source: Facebook

A ganawar da za’ayi yau, za’a fayyace muhawara kan tsarin zaben fidda gwanin da jam’iyyar za tayi amfani da shi wajen zaben wadanda zasu wakilceta a zaben 2019.

Wasu sanatocin jam’iyyar sun bayyanawa jaridar Premium Times a ranan Laraba cewa za su iya barin jam’iyyar idan akayi amfani da tsarin kullaliyar zabe.

Sanatocin a tsoron cewa gwamnonin za suyi amfani da hakan wajen juya zaben ga wadanda suke so a jihohinsu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel