Gwamnatin Legas zata dauki sama da malamai 2,000 aiki a ranar Juma'a

Gwamnatin Legas zata dauki sama da malamai 2,000 aiki a ranar Juma'a

- Gwamnatin jihar Legas zata fara daukar malamai 2,000 daga ranar juma'a 31 ga watan Augusta

- Gwamnan jihar ya ce daukar ma'aikatan zai bada damar cike gurbin karancin malamai da ake dasu a makarantun gwamnatin jihar

- Malaman da za'a dauka aikin, zasu koyar ne a makarantun firame da sakandire da ke a kananan hukumomi 20 na jihar

Gwamnatin jihar Lagas ta ce a shirye take tsaf don daukar sama da malamai 2,000 aiki, da zasu koyar a makarantun firamare da sakandire na jihar. Malaman da za'a dauka aikin, za'a turasu ne makarantun firame da sakandire mallakin gwamnatin jihar da ke a kanan hukumomi 20 na jihar.

Gwamnan jihar ta Legas, Akinwunmi Ambode ya sanar da bukatar daukar karin malaman a wani taron jin ra'ayoyin al'uma da ya gudana a Ibeju Lekki, dake jihar.

Akinwunmi ya ce : "Gwamnatin jihar Legas ta shirya don daukar malamai 1,000 da zasu yi koyar a makarantun firamare, da kuma malamai 1,200 da zasu koyar a makarantun sakandire, inda za'a fara tantance wadanda za'a dauka daga karfe 12:00 na daren ranar Juma'a, 31 ga watan Augusta, zuwa karfe 12:00 na daren Alhamis, 6 ga watan Satumba."

KARANTA WANNAN: Hukumar INEC tasha alwashin gurfanar da duk wanda ta samu da laifin siyen kuri'u

Ambode ya kuma yi alkawarin cewa gwamnatinsa zata ci gaba da daukar malamai aiki, don cike gurbin rashin malamai da wasu makarantun gwamnati na jihar ke yi, musamman ganin yadda ake samun karuwar dalibai a makarantun gwamnati.

Haka zalika a wannan taro, mataimakiyar gwamnan jihar, Idiat Adebule, ta ce daukar aikin zai taimaka wajen bunkasa fannin koyo da koyarwa a jihar.

Ta kara da cewa makarantun gwamnati na ci gaba da samun karuwar dalibai a cikin shekaru uku, biyo bayan inganta gine ginen makarantun da kuma samar da walwala ga malamai da kuma ma'aikatan fannin.

Ana sanar da masu sha'awar shiga aikin, da su cike bukatar hakan a shafin daukar aiki na gwamnatin da ke a yanar gizo.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel