Dalilin tsada da karancin shinkafa 'yar gida – Gwamnati

Dalilin tsada da karancin shinkafa 'yar gida – Gwamnati

- Maikatar gona ta bayyana dalilin tsada da karancin shinkafa 'yar gida a kasuwa

- Ta daura laifin akan tsarin raba shinkafar daga masu cashe ta zuwa kasuwa

- Masu casar shinkafa na dora alhakin tsadar ta gida a kan tsadar kayan aiki da kuma tsadar aikin casa da gyaran ta

Ma’aikatar Harkokin Gona da Raya Karkara, ta dora laifin tsadar shinkafa yar gida da karanci da tayi akan matsalar tsarin raba shinkafar daga masu cashe ta zuwa kasuwa.

Mataimakiyar daraktar lura da safarar shinkafa, Fatimah Aliyu ce ta sanar da hakan a ranar Laraba, 29 ga watan Agusta a babban birnin tarayya, Abuja.

Ta yi jawabi kan hakan ne a wajen taron shekara-shekara, na biyu na Gidauniyar A. Kufour Foundation (JAKF) ta gudanar.

Dalilin tsada da karancin shinkafa 'yar gida – Gwamnati

Dalilin tsada da karancin shinkafa 'yar gida – Gwamnati
Source: Facebook

Ta ce kasuwar shinkafar cikin gida na samun karbuwa sosai, sai dai kuma su masu cashe shinkafar na tsoron tula shinkafar kasuwanni ne, saboda tsoron karyewar farashi idan ta yi cimbu saboda gasa tsakanin ‘yan kasuwa masu shigo da shinkafar waje.

Ta ce su na gujema karyewar darajar shinkafar gida ne idan aka kwatanta da ta waje, shi ya sa masu cashe ta ke baya-baya da raba ta cikin kasuwanni har ta wadata.

KU KARANTA KUMA: 2019: Matasan Arewa sun tsayar da Saraki a matsayin shugaban kasa

Ta ce sannan kuma wasu na cewa shinkafar da ake shigowa da ita daga waje ta ma fi ta gida saukin farashi da rahusa.

Su kuma masu casar shinkafa na dora alhakin tsadar ta gida a kan tsadar kayan aiki da kuma tsadar aikin casa da gyaran ta, matsalar rashin dawwamammiyar wutar lantarki, tsadar sufuri ko jigilar shinkafar zuwa kasuwanni da kuma fasa-kwaurin da ake yin a shinkafar waje.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel