2019: Sheriff bai da muradin tsayawa takarar kowani kujera – Kungiya

2019: Sheriff bai da muradin tsayawa takarar kowani kujera – Kungiya

- Wata kungiya ta bayyana cewa Ali Modu Sheriff bai da ra'ayin takarar kowani matsayi a zabe mai zuwa

- Hakan raddi ne ga ikirarin tsohon mataimakin jihar Borno dake cewa Sheriff na son takarar shugabancin kasa

- Sakataren kungiyar yace Sheriff ya koma APC ne don ya ga cewa Shugaba Buhari mutun ne mai mutunci

Shugaban kungiyoyin magoya bayan shugaban kasa Buhari na 2019, Sanata Ali Modu Sheriff bai da muradin tsayawa takarar kowani kujera a zabe mai zuwa, kamar yadda kungiyar magoya bayansa ta fadi.

Sakatarenkungiyar, Kassim Muhammed Kassim, a wata sanarwa a jiya Laraba, 29 ga watan Agusta ikirari daban-daban da tsohon mataimakin gwamnan jihar Borno, Alhaji Shettima Yuguda Dibal yayi akan Sheriff ba gaskiya bane don haka kada a saurare shi.

Yace: “Sheriff bai koma jam’iyyar APC son takarar kujerar shugabancin kasa ko kuma ya tsayar dad an takarar gwamna a jihar Borno ba. Bai sauya sheka don takarar ko wani matsayi ba, sai dai yayi hakan ne akan kudirin bayar da nasa gudunmawar wajen gyara kasar da kuma kawo kwarewarsa da kuma magoya bayansa a fadin jihohi 36 na tarayyar kasar."

2019: Sheriff bai da muradin tsayawa takarar ko wani kujera – Kungiya

2019: Sheriff bai da muradin tsayawa takarar ko wani kujera – Kungiya
Source: Depositphotos

Kassim ya kara da cewa ikirarin da Dibal yayi cewa Sheriff ya koma APC saboda ya rasa shugabancin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ba gaskiya bane.

Sabanin sauran tsoffin mambobin APC da suka sauya sheka zuwa wata jam’iyya dauke da kudirin neman kujerar mulkin kasar, Sheriff ya sauya sheka zuwa APC ne saboda ya ga cewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari mutum ne mai mutunci wadda bai damu da abunda zai samu ba.

Ikirarin cewa Sheriff na son yiwa Shugaba Buhari da Oshiomhole cin mutunci ne ga shugabannin biyu aa cewar kungiyar.

KU KARANTA KUMA: Sabon bayani ya billo akan makomar korarren shugaban DSS Daura

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Ibrahim Hassan Dankwambo, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Democratic Party (PDP) kuma gwamnan jihar Gombe, ya bayyana cewa baya siyasar ko a mutu ko ayi rai don kawai ya zama dan takara a jam’iyyar a zaben 2019.

Dankwambo, yayinda yake neman goyon bayan mambobin jam’iyyar da diligit akan kudirinsa na son zama dan takarar jam’iyyar a zabe mai zuwa a ranar Laraba, 29 ga watan Agusta, a Benin, jihar Edo yace zai goyama duk wadda ya zamo dan takara baya idan har aka yi adalci da gaskiya wajen zaben.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel