Ba na siyasar ko a mutu ko ayi rai – Dankwambo

Ba na siyasar ko a mutu ko ayi rai – Dankwambo

- Gwamnan jihar Gombe, Dankwambo yace baya siyasar ko a mutu ko ayi rai

- Ya sha alwashin marawa duk wanda yayi nasarar samun tikitin takarar shugabancin kasa a PDP idan dai har akayi adalci wajen zaben

- Dankwambo dai ya nuna aniyarsa na son takarar shugaban kasa a zaben 2019

Ibrahim Hassan Dankwambo, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Democratic Party (PDP) kuma gwamnan jihar Gombe, ya bayyana cewa baya siyasar ko a mutu ko ayi rai don kawai ya zama dan takara a jam’iyyar a zaben 2019.

Dankwambo, yayinda yake neman goyon bayan mambobin jam’iyyar da diligit akan kudirinsa na son zama dan takarar jam’iyyar a zabe mai zuwa a ranar Laraba, 29 ga watan Agusta, a Benin, jihar Edo yace zai goyama duk wadda ya zamo dan takara baya idan har aka yi adalci da gaskiya wajen zaben.

Wata kungiya ta bukaci Gwamna Dankwambo da ya yi takarar kujerar shugabancin kasa a 2019. Kungiyar ta Dankwambo Grassroots Networks (DGN) ta bayyana gwamnan a matsayin dan takara daya da ya dace da takara a 2019.

Ba na siyasar ko a mutu ko ayi rai – Dankwambo

Ba na siyasar ko a mutu ko ayi rai – Dankwambo
Source: Depositphotos

Ku tuna cewa bayanai sun billo a ranar Lahadi, 12 ga watan Agusta kan cewa an matsawa gwamnan na jihar Gombe da ya ajiye kudirinsa gabannin zaben fidda gwani na jam’iyyar.

KU KARANTA KUMA: Sabon bayani ya billo akan makomar korarren shugaban DSS Daura

Dankwambo wadda ya bayyana kudirinsa na takarar shugabancin kasa a wata daya da ya gabata na fuskantar matsin lamba daga wasu shugabannin siyasa da sarakuna daga yankin arewacin kasar kan ya janye ma gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal.

Gwamnan na jihar Gombe wadda ke neman takara a zaben 2019 ya yanki fam din takarar shugaban kasa inda ya biya naira miliyan 12.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa kungiyar matasan Arewa mai suna Northern Youths for Peace and Security (NYPS), a jiya Laraba, 29 ga watan Agusta sun tsayar da shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki a matsayin zabinsu na takarar kujerar shugaban kasa a zabe mai zuwa.

Shugaban kungiyar, Salisu Magaji, ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Jalingo, babban birnin jihar Taraba, bayan wani ganawa tare da manyan matasan arewa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel