Ina nan daram a jam'iyyar PDP ko da na rasa Tikitin takara - Sule Lamido

Ina nan daram a jam'iyyar PDP ko da na rasa Tikitin takara - Sule Lamido

Tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma manemin takarar kujerar shugaban kasa a jam'iyyarr PDP, Alhaji Sule Lamido, ya bayyana cewa zai ci gaba da kasancewa a jam'iyyar ko da ya rasa tikitin takara na jam'iyyar a yayin zaben fidda gwani.

Alhaji Lamido ya bayyana hakan ne yayin ganawar sa da manema labarai a ranar Larabar da ta gabata yayin wata ziyarar bazata da ya kai gidan Janar Jeremiah Useni dake birnin Jos na jihar Filato.

A bayan can kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, tsohon gwamnan ya ziyarci shelkwatar jam'iyyar ta PDP dake jihar Filato inda ya bayyana kudirin sa karara na tsayawa takara kujerar shugaban kasa a zaben 2019.

Sai dai tsohon gwamnan ya bayyana cewa dukkanin manema tikitin takara na jam'iyyar su na daidai da juna kuma kowanen su na da cikakkiyar cancanta ta jagorantar kasar nan ta Najeriya.

Ina nan daram a jam'iyyar PDP ko da na rasa Tikitin takara -Sule Lamido

Ina nan daram a jam'iyyar PDP ko da na rasa Tikitin takara -Sule Lamido
Source: UGC

Lamido ya kuma bayyana cewa zai goyi bayan duk wani dan takara da jam'iyyar ta fitar a matsayin gwanin fafatawa a zaben 2019 domin kuwa dukkanin su na da kudiri daya na ci gaban kasar nan.

KARANTA KUMA: 2019: Za a gudanar da zaɓe na gaskiya da adalci - Shugaba Buhari ya sha alwashi ga Firai Ministar Birtaniya, Theresa May

Kazalika tsohon gwamnan ya kuma musanta jita-jitar cewa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ke daukar nauyin takarar sa ta kujerar shugaban kasa, inda ya ce ko kadan ba ya da wani Ubangida a faggen siyasa.

Legit.ng ta fahimci cewa, Lamido zai bayar da muhimmanci wajen kawo karshen matsalolin tsaro musamman rikicin makiyaya da manoma dake ci gaba da aukuwa a wasu sassa na kasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel