2019: Matasan Arewa sun tsayar da Saraki a matsayin shugaban kasa

2019: Matasan Arewa sun tsayar da Saraki a matsayin shugaban kasa

- Kungiyar matasan Arewa sun amince da Bukola Saraki a matsayin takarar shugaban kasa a 2019

- Sun bayyana cewa Saraki ne zai iya ceto kasar daga halin da take ciki

- Kungiyar tace gwamnati mai ci ta gazawa al'umman Najeriya

Kungiyar matasan Arewa mai suna Northern Youths for Peace and Security (NYPS), a jiya Laraba, 29 ga watan Agusta sun tsayar da shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki a matsayin zabinsu na takarar kujerar shugaban kasa a zabe mai zuwa.

Shugaban kungiyar, Salisu Magaji, ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Jalingo, babban birnin jihar Taraba, bayan wani ganawa tare da manyan matasan arewa.

2019: Matasan Arewa sun tsayar da Saraki a matsayin shugaban kasa

2019: Matasan Arewa sun tsayar da Saraki a matsayin shugaban kasa
Source: Depositphotos

Magaji ya bayyana cewa shawarar da kungiyar ta yanke ya kasance akan yadda da tayi da cewa gwamnati mai ci ta gaza sosai sannan kuma cewa Saraki ne mutum da ake ganin yana da abunda ake bukata don ceto Najeriya daga halin da take ciki.

KU KARANTA KUMA: CBN ta ci tarar bankuna 4 N5.8bn, ta umurci masu aro da MTN da su dawo da $8.1bn

Kungiyar tan ace kan cewa lallai Saraki ya kafa tariyi lokacin da yayi gwamnan jihar Kwara sannan kuma cewa yadda yake tafiyar da majalisar dattawa a matsayinsa na shugaba ya nuna cewa shine dan takara da ya kamata jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) da yan Najeriya su yarje mawa domin ceto kasar.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma daya daga cikin masu neman tikitin takarar shugabancin kasa a inuwar jam'iyyar PDP a 2019, Sule Lamido ya ce tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo yana goyon bayansa dari bisa dari.

Daily Trust ta ruwaito cewa tsohon gwamnan ya yi wannan magana ne a ranar Laraba 29 ga watan Augusta a garin Jos na jihar Plateau.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel