Abinda ya sa Obasanjo ke son in zama shugaban kasa - Lamido

Abinda ya sa Obasanjo ke son in zama shugaban kasa - Lamido

- Mai neman takarar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar PDP, Sule Lamido ya ce tsohon shugaban kasa Jonathan yana goyon bayansa

- A cewarsa Jonathan yana goyon bayansa ne saboda ya lura shi mai kwazo da himma ne kuma yana kishin Najeriya

- Ya kuma ce ba zai fice daga jam'iyyar PDP ko da bai samu nasarar zama dan takarar jam'iyyar ba bayan zaben fitar da gwani

Tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma daya daga cikin masu neman tikitin takarar shugabancin kasa a inuwar jam'iyyar PDP a 2019, Sule Lamido ya ce tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo yana goyon bayansa dari bisa dari.

Daily Trust ta ruwaito cewa tsohon gwamnan ya yi wannan magana ne a ranar Laraba 29 ga watan Augusta a garin Jos na jihar Plateau.

Abinda ya sa Obasanjo ke son in zama shugaban kasa - Lamido

Abinda ya sa Obasanjo ke son in zama shugaban kasa - Lamido
Source: UGC

Ya bayyana cewa Obasanjo ya same shi a jam'iyyar PDP ne amma Obasanjo ya lura cewa shi mutum ne mai jajircewa da kwazo da himma.

DUBA WANNAN: Gargadi: Jihohin Najeriya 7 zasu fuskanci ambaliyar ruwa - NIHSA

Ya ce: "Obsanjo ya same ni a PDP ne amma daga baya ya zama shugaban kasa na sai dai duk da haka ya lura cewa ni mutum ne mai kwazo da himma da kaunar cigaban Najeriya. Hakan yasa ya ke goyon baya na."

Lamido ya ce ba zai fice daga jam'iyyar PDP ba ko da baiyi nasarar lashe zaben fitar da gwani ba saboda duk wanda ya yi nasarar zaiyi aiki ne bisa tsarin da aka gina jam'iyyar a kai.

Ya kara da cewa, "A jam'iyyar PDP akwai miliyoyin 'yan jam'iyya masu ra'ayi irin na Sule Lamido da Wike da Fayose da Dankwambo da Darius Ishaku amma duk halayensu daya ne wajen akidun siyasa ba kamar APC ba wanda mutum daya ne kawai a jam'iyyar duk sauran tarin iska ne."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel