Dalilin zuwan Shugabar Jamus Merkel kasar nan Inji Ambasada Tuggar

Dalilin zuwan Shugabar Jamus Merkel kasar nan Inji Ambasada Tuggar

Jakadan Najeriya a Kasar Jamus Yusuf Tuggar ya bayyana dalilin da zai kawo Shugabar Kasar Jamus bayan zuwa Shugabar Birtaniya Najeriya. A makon nan ne Najeriya za ta karbi bakuncin Shugabannin.

Dalilin zuwan Shugabar Jamus Merkel kasar nan Inji Ambasada Tuggar

Ambasada Tuggar Jakadan Najeriya a kasar Jamus yace May za ta ga Buhari
Source: Depositphotos

Yusuf Tuggar ya bayyana cewa Shugabar Jamus Angela Merkel za ta kawo ziyara Najeriya ne domin tattauna alakar da ta shafi harkar noman abinci da kuma tattalin arziki da tsaro tsakanin Najeriya da kuma kasar ta Turai.

A Ranar Juma’a ne Shugaban ta Jamus za ta zo Najeriya inda kuma za ta gana da Shugaban kasa Muhammadu Buhari. Takwarar Shugaba Buhari za ta zo Najeriya ne saboda maganar alakar kasuwancin da ke tsakanin kasahen.

KU KARANTA: Tsohon Shugaban DSS Daura yayi magana bayan korar sa daga aiki

Ambasadan ya bayyana wannan ne a wajen wata hira da aka yi a babban Birnin Tarayya Abuja inda yace tattaunawar Shugabannin za ta taimaka wajen cigaban Yankin Arewa maso Gabashin Najeriya da rikicin Boko Haram ya aukawa.

Ganawar za ta zo ne lokaci kadan bayan Shugaba Buhari ya gana da Firayim Ministar Ingika Theresa May jiya a Abuja. Akwai kuma alaka ta ilmi da koyar da ma’aikatan Najeriya sanin aiki tsakanin Najeriya da Kasar Jamus tun ba yau ba.

A jiya dai Sanatan Najeriya Rabiu Musa Kwankwaso ya aikawa Theresa May goron gayyata wajen taron kaddamar da shirin tsayawa takarar Shugaban kasa da yayi a Abuja inda ya sha alwashin tika Buhari da kasa a zaben 2019 domin ceto Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Mailfire view pixel