Sabon bayani ya billo akan makomar korarren shugaban DSS Daura

Sabon bayani ya billo akan makomar korarren shugaban DSS Daura

Rahotanni sun kawo cewa sabon bayani ya billo game da tsohon mai ba kasa shawara a harkar tsaro, Lawal Daura, wadda mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya dakatar.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa duk da cewar Daura na a tsare, an bashi damar ganawa da matayensa da kuma wasu hadimansa.

An tattaro craw tsohon shugaban na DSS na jiran hukuncin da Shugaban asa Muhammadu Buhari zai yanke akansa.

Sabon bayani ya billo akan makomar korarren shugaban DSS Daura

Sabon bayani ya billo akan makomar korarren shugaban DSS Daura
Source: Depositphotos

Wata majiya tace: “Tsohon shugaban DSS na nan a killace a wani gida amma yana samun damar ganin matayansa, yara da kuma hadimansa. Bai san tanadin da fadar shugaban kasa tayi masa ba. Yana jiran hukuncin Shugaba Buhari akan sa.

KU KARANTA KUMA: 2019: Ko kuri’u miliyan 12 cikakke Buhari ba zai samu ba a Arewa – Turaki

“Burinsa shine Shugaban kasa da Yan Najeriya su saurari nasa bangaren kan abunda ya afku a ranar 7 ga watan Agusta. An hana shi fita a yanzu. Yana son komawa gidansa.

“Sai dai ana sauraron ganin yadda Shugaban kasar zai magance lamarin. Ina ganin yana sauraron rahoto daga mataimakin shugaban kasa da IGP.

“Dukkanin jami’ai, hadda ministoci na guje ma tattaunawa akan Daura saboda kada a zarge su da bangarenci.

“Duk mun banbanta akan lamarin nan amma mun bar ma zuciyoyinmu ra’ayinmu. Bamu san ra’ayin shugaban kasar ba.”

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel