Ba yunkurin murde zabe ta sa Jonathan ya kori Sulaiman Abba ba - Omokri

Ba yunkurin murde zabe ta sa Jonathan ya kori Sulaiman Abba ba - Omokri

Tsohon Shugaban Kasa Dr. Goodluck Jonathan ya maidawa tsohon Shugaban ‘Yan Sandan Najeriya Sulaiman Abba martani bayan ya zarge sa da yunkurin amfani da shi wajen murde zabe a 2015.

Ba yunkurin murde zabe ta sa Jonathan ya kori Sulaiman Abba ba - Omokri

Omokri yace tsohon Shugaban ‘Yan Sanda Abba makaryaci ne
Source: Depositphotos

Reno Omokri wanda tsohon Hadimin Goodluck Jonathan ne, ya takawa IGP Sulaiman Abba mai ritaya burki na zargin tsohon Shugaban kasar da kokarin amfani da ‘Yan Sanda wajen murde zaben Gwamna da aka yi a Jihar Osun a 2014.

Omokri wanda ya ke ba Shugaba Jonathan shawara a wancan lokaci yace an yi waje da Sulaiman Abba ne saboda kashe wani babban Jami’in zabe da iyalin sa da aka yi a Jihar Kano yayin da Shugaban ‘Yan Sandan ya gaza yin komai.

KU KARANTA: Tsohon Shugaban kasa Jonathan ya jinjinawa Bukola Saraki

Tsohon mai ba Shugaban kasar shawara yace Jonathan ya sallami Sufeta Janar Sulaiman Abba daga aiki ne kusan fiye d watanni 7 bayan an yi zaben Gwamna a Osun. Omokri yace hakan ya nuna tsohon Shugaban ‘Yan Sandan makaryaci ne.

Reno Omokri yace idan har saboda maganar murde zaben Osun ne aka kori Abba, babu yadda za ayi Jonathan ya bar sa a kan kujerar sa har bayan zaben Shugaban kasa a 2019. Omokri a jawabin na sa yace babu gaskiya a zance na tsohon IGP.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel