2019: Ko kuri’u miliyan 12 cikakke Buhari ba zai samu ba a Arewa – Turaki

2019: Ko kuri’u miliyan 12 cikakke Buhari ba zai samu ba a Arewa – Turaki

- Turaki ya kalubalanci masu ikirarin cewa Shugaba Buhari zai samu kuri'u muliyan 12 daga Arewa

- A cewarsa wannan zamanin ya shige

- Dan takarar shugaban kasar yace yan Najeriya sun rigada sun dawo daga rakiyar gwamnatin APC

- Ya ce kuncin rayuwar da mutane ke ciki na rashin abinci ba zai sa su jefa kuri'unsu ga wanda ya saka su a cikin halin ba

Tsohon ministan ayyuka na musamman kuma dan takarar kujerar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Kabiru Tanimu Turaki, ya bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari ba zai iya samun kuri’u miliyan 12 ba daga Arewa a zaben 2019.

Turaki, wadda ya yanki fam din takara a babban sakatariyar PDP dake Abuja a ranar Laraba, 29 ga watan Agusta yace ikirarin cewa lokaci ya karyata ikirarin da ake yi na cewa Buhari ya rigada ya samu kuri’u miliyan 12 daga Arewa.

2019: Ko kuri’u miliyan 12 cikakke Buhari ba zai samu ba a Arewa – Turaki

2019: Ko kuri’u miliyan 12 cikakke Buhari ba zai samu ba a Arewa – Turaki
Source: Facebook

Tsohon ministan wadda ya samu wakilcin daraktan gangamin zaben sa, Sola Atere yace: “Abunda suke ke fadi kawai abune day a faru a baya a 2015. Abubuwa sun chanja. Idan baka hau mulki ba, kana iya yin duk wani tatsuniya. A yanzu kidin ya chanja. Yan Najeriya sun ga irin rawar ganin da gwamnatin APC zata iya takawa.

“Sannan idan kayi duba ga ayyuka da dama duk ikirarin karya ne, PDP ce ta samar da su. Wannan gwamnati ce da take ta tafka kurakurai a kowani lokaci. Yan Najeriya sun san duk wadannan abubuwan. Kuri’u miliyan 12 da suke ikirari ya sauka.

KU KARANTA KUMA: An kama wata mahaukaciyar bogi da jikin ‘Dan Adam a Legas

“Saboda idan kayi duba ga lamarin tattalin arziki, inda mutane suke korafin cewa basa iya samun abinci sau daya a rana, ta yaya kuke tunanin zasu fito su jefe kuri’u har miliyan 12 ga mutumin da ya haddasa masu wannan matsala?.”

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel