PDP: Bafarawa ya yi watsi da duk wani tayin sulhu da sauran yan takarar shugaban kasa

PDP: Bafarawa ya yi watsi da duk wani tayin sulhu da sauran yan takarar shugaban kasa

Tsohon gwamnan jahar Sakkwato kuma dan takarar shugabancin Najeriya a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, Attahiru Dalhatu Bafarawa ya bayyana cewa abinda yafi shine a kada zaben fidda gwani a tsakanin yan takarkarun shugaban kasa dake PDP.

Legit.ng ta ruwaito Bafarawa yana cewa babu bukatar a shiga wani maganan yin sulhu a tsakanin yan takarkarun shugaban kasa da suka fito daga jam’iyyar PDP sakamakon adadinsu na kara yawa.

KU KARANTA: Rayukan mutane 8 da gidaje 95 sun salwanta a wani hari da aka kai jahar Filato

Bafarawa ya bayyana haka ne jim kadan bayan ya sayi takardar nuna sha’awa tsayawa takarar shugaban kasa a sakatariyar PDP, inda yace duba da yawan yan takarar jam’iyyar PDP, hakan na nuna jam’iyyar na kara karfi a kullum.

PDP: Bafarawa ya yi watsi da duk wani tayin sulhu da sauran yan takarar shugaban kasa

Bafarawa
Source: Depositphotos

“Babu bukatar yin sulhu, kamata yayi a gudanar da zaben fidda gwani, sai a mara ma duk wanda ya samu nasara baya don mu tabbatar mun kayar da jam’iyyar APC da shugaban kasa Buhari a zaben 2019.” Inji shi.

A wani labarin kuma, da yammacin Laraba 29 ga watan Agusta bayan kammala taron kaddamar da takarar shugaban kasa na tsohon gwamnan jahar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, uwar jam’iyyar PDP ta kira dukkanin yan takaranta wata ganawar sirri.

Sai dai masana al’amuran siyasa na ganin wannan ganawa baya rasa nasaba da ganin dubun dubatan jama’an da suka halarci taron kaddamarwar na Kwankwaso, wanda hakan ya nuna yana da jama’a, shi yasa aka kira taron yan takarar don yin sulhu.

Zuwa yanzu PDP nada yan takarar shugaban kasa da suka hada da Atiku Abubakar, Ahmed Makarfi, Sule Lamido, Rabiu Kwankwaso, Tanimu Turaki, Attahiru Bafarawa, Datti Baba Ahmed, Ibrahim Shekarau, da Aminu Waziri Tambuwal.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel