Rayukan mutane 8 da gidaje 95 sun salwanta a wani hari da aka kai jahar Filato

Rayukan mutane 8 da gidaje 95 sun salwanta a wani hari da aka kai jahar Filato

Ana cikin zaman dar dar sakamakon tashin hankula da aka samu yayin da wasu mahara suka kai farmaki ga wasu kauyukan Abonong da Zayit dake cikin yankunan Foron na karamar hukumar Barikin Ladi na jihar Filato.

Kaakakin rundunar Yansandan jahar, Terna Tyopev ne ya sanar da haka a ranar Laraba, 29 ga watan Agusta, inda yace maharan sun kai farmaki zuwa kauyukan ne da sanyin safiyar Laraba.

KU KARANTA: Dukkan mai rai mamaci ne: Yadda wani Alhajin Najeriya ya gamu da ajalinsa a Makka

Legit.ng ta ruwaito an saci sama da shanu dari uku da goma, 310 a yayin wannan farmaki da aka kai, sai dai ga sanarwar da rundunar Yansandan jahar ta fitar ta bakin Kaakakin nata:

“A lokacin da muka rahoton harin da aka kai kauyukan Abonong da Zayit bamu bata lokaci wajen tura jami’anmu ba.

“Amma yayin da muke tunkarar kauyukan, sai maharan suka hangemu, nan da nan suka ranta ana kare, da muka shiga kauyukan mun gano sun kashe mutane takwas, sun kona gidaje 95 tare da sace shanu 310. Da” Inji Terna Tyopev.

Kaakakin ya cigaba da cewa: “Bugu da kari maharan sun saci buhuhunan hatsi, sa’annan suka barnata dukiyoyi na miliyoyin nairori, amma har yanzu jami’anmu sun mamaye yankunan don gudun sake kai wasu sabbin hare hare.”

Idan za’a tuna a kwanakin baya ne aka samu wani jarumin Limamin daya ceci kiristoci yan kabilan Berom har sama dari uku daga hannun yan bindigan da suka yi kokarin yi musu kisan kare dangi, inda ya boyesu a cikin Masallaci da gidansa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel