Saraki: An sake gargadin Jam'iyyar APC ta bi dokar kasa wajen tsige Shugaban Majalisa

Saraki: An sake gargadin Jam'iyyar APC ta bi dokar kasa wajen tsige Shugaban Majalisa

Wasu manyan Lauyoyin Najeriya da ake ji da su sun shawarci Jam’iyyar APC ta bi dokar kasa wajen yunkurin da ta ke yi na tsige Bukola Saraki daga matsayin sa na Shugaban Majalisar Dattawa.

SarakI: An sake gargadin Jam'iyyar APC ta bi dokar kasa wajen tsige Shugaban Majalisa

An gargadi Jam'iyyar APC game da sauke Shugaban Majalisar Dattawa
Source: Depositphotos

Jaridar Punch ta rahoto cewa manyan Lauyoyin Najeriya irin su Farfesa Fidelis Oditah SAN, Roland Otaru SA da kuma Cif Joe-Kyari Gadzama SAN duk sun nemi Jam'iyyar APC ta bi tsarin mulki wajen sauke Bukola Saraki daga kujerar sa.

Wadannan manyan Lauyoyi sun bayyana ra’ayin su game da shirin tsige Saraki inda su ka tabbatarwa APC cewa dole ta samu ‘Yan Majalisu akalla 73 kafin ta iya cire Dr. Bukola Saraki daga mukamin sa ganin cewa ya sauya-sheka.

Gadzama wanda babban Lauya ne ya nuna cewa APC na kokarin amfani da ‘Yan Majalisun da su ka halarci zaman da za ayi idan aka bude Majalisa wajen tsige Saraki inda yace hakan ya saba doka kuma dole a samu sa hannun Sanatoci 73.

KU KARANTA: APC ta maidawa Saraki martani bayan yace bai tsoron a tsige sa

Roland Otaru ma dai ya tabbatar da hakan inda yace ba za a iya tunbuke Shugaban kasa da Mataimakin sa da kuma Shugaban Majalisar Dattawa daga kujera ba har sai an samu kashi 2 cikin 3 na Majalisar Tarayya tayi na’am da wannan shiri.

Fidelis Oditah ya tunawa APC cewa ba yau aka fara tsige Shugabannin Majalisar Dattawa ba kuma a ko yaushe sai da 2/3 na Majalisa ta amince. A baya an tsige Evan Enwerem da Chuba Okadigbo a Majalisar Dattawan Kasar inji wannan babban Lauya.

Haka nan wani Hadimin Goodluck Jonathan a lokacin yana kan mulki watau Dr. Doyin Okupe ya bayyana cewa dole a bi dokar kasa wajen taba Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel