Firaministar Ingila ta gana da Dangote, Otedola da Adenuga a Legas

Firaministar Ingila ta gana da Dangote, Otedola da Adenuga a Legas

- Firaministar kasar Ingila ta koma Legas domin ganawa da Dangote da manyan 'yan kasuwar Najeriya

- Theresa May ta koma Legas ne domin ganawa da kungiyoyin 'yan kasuwar Najeriya

- Gwamnan jihar Legas, Akinwumi Ambode, ne ya tarbi Firaministar bayan ta sauka a Legas din

Majiyar Legit.ng ta sanar da ita cewar bayan Dangote, manyan 'yan kasuwa irinsu Femi Otedola, Mike Adenuga da sauran su zasu halarci taron da Theresa May din zata yi da 'yan kasuwar.

Yayin ganawar ta shugaba Buhari a Abuja, Najeriya da kasar Ingila sun saka hannu kan yarjejeniyar hadin gwuiwa a kan harkokin tsaro da bunkasa tattalin arziki.

Firaministar Ingila ta gana da Dangote, Otedola da Adenuga a Legas

Firaministar Ingila ta gana da Dangote, Otedola da Adenuga a Legas
Source: Twitter

Theresa May ta ziyarci Najeriya ne a cigaba da rangadin kasashen Afrika da take yi.

DUBA WANNAN: An kone Fasto, matar sa da 'ya'yansa a bainar jama'a a sabon rikicin Barkin Ladi

A jiya, Talata, ne Theresa May, firaministar kasar Ingila ta ce Najeriya ce yanzu haka a sahun gaba a yawan talakawa a duniya. Da take Magana jiya, Talata, a birnin Cape Town na kasar Afrika ta Kudu, Theresa May ta bayyana cewar nahiyar Afrika ce a gaba wajen yawan mutanen da rigingimu suka raba da muhallinsu.

Har ila yau ta kara da cewa nahiyar Afrika ce a gaba wajen yawan talakawa a duniya, tare da bayyana cewar a kalla mutane kimanin miliyan 87 ne ke fama da matsanancin talauci a Najeriya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel