Ba don shugabanci irin na Saraki ba, da majalisar dokoki ta kasance cikin hargitsi – Jonathan

Ba don shugabanci irin na Saraki ba, da majalisar dokoki ta kasance cikin hargitsi – Jonathan

- Cikakken bayanin ganawar Saraki da Jonathan ya billo

- Saraki yace ya kai ziyara ga tsohon shugaban kasar ne domin nuna girmamawa a gare shi sannan ya sanar masa da komawarsa PDP

- Jonathan ma yayi amfani da damar wajen yaba ma tsarin shugabanci na Saraki a majalisar dokokin kasar

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yabama shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki a ranar Laraba, 29 ga watan Agusta kan irin shugabanci da yake gudanarwa a majalisar dokokin kasar.

Jonathan yayi Magana ne a lokacin da Saraki ya kai masa ziyarar ban girma a ofishinsa na Maitama, Abuja, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Legit.ng ta tattaro cewa tsohon shugaban kasar yace irin goyon bayan da Saraki ke samu daga yan majalisu na majalisar dattawa da na wakilai ya isa ya nuna kwarewarsa wajen shugabanci.

Da farko dai Saraki yace ziyarar da ya kaiwa tsohon shugaban kasar na ban girma ne sannan ya sanar masa da dawowarsa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Ba don shugabanci irin na Saraki ba, da majalisar dokoki ta kasance cikin hargitsi – Jonathan

Ba don shugabanci irin na Saraki ba, da majalisar dokoki ta kasance cikin hargitsi – Jonathan
Source: Twitter

A wani lamari na daban mun ji cewa wasu sanatoci sunyi barazanar barin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) idan har jam’iyyar taki daukar matakin yin zaben fidda gwani kai tsaye don zabukan 2019, jaridar Premium Times ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Kwankwaso ya sha alwashin kayar da Buhari a zaben 2019

Majiyarmu ta tattaro cewa wasu yan majalisa sunyi gargadin cewa jam’iyyar zata sake fuskantar sauya sheka na baki daya idan har taki bin wannan tsari na gudanar da zaben fidda gwani.

Sun yi zargin cewa wasu gwamnoni na matsawa shugaban jam’iyyar lamba kan cewa yayi amfani da akasin haka ta hanyar zaben dan takara ba tare da zaben fidda gwani ba a 2019.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel