2019: Za a gudanar da zaɓe na gaskiya da adalci - Shugaba Buhari ya sha alwashi ga Firai Ministar Birtaniya, Theresa May

2019: Za a gudanar da zaɓe na gaskiya da adalci - Shugaba Buhari ya sha alwashi ga Firai Ministar Birtaniya, Theresa May

A ranar yau ta Laraba shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayar da tabbacin sa ga Firai Ministar Birtaniya, Theresa May, cewa gwamnatinsa ta dukufa wajen tabbatar da gudanar da zabe na adalci da gaskiya a shekarar 2019.

Cikin wata sanarwa da sa hannun kakakin shugaban kasa, Mista Femi Adesina, shugaba Buhari ya bayyana hakan ne yayin ganawar sa da Firai Ministar ta Birtaniya a fadar sa ta Villa dake babban birnin kasar nan na Abuja.

Shugaba Buhari ya kuma yi lale maraba tare da yabawa Kasar Birtaniya dangane da goyon bayan karfafa dimokuradiyyar gami da yakar cin hanci da rashawa a kasar nan.

2019: Za a gudanar da zaɓe na gaskiya da adalci - Shugaba Buhari ya sha alwashi ga Firai Ministar Birtaniya, Theresa May

2019: Za a gudanar da zaɓe na gaskiya da adalci - Shugaba Buhari ya sha alwashi ga Firai Ministar Birtaniya, Theresa May
Source: Facebook

Legit.ng ta ruwaito cewa, a yau ne Firai Ministar ta ziyarci shugaban kasa Buhari inda a yayin bankwana da kasar Najeriya ta yada zango a jihar Legas inda ta gana da gwamnan jihar, Akinwunmi Ambode da kuma fitaccen attajirin nan, Alhaji Aliko Dangote.

KARANTA KUMA: Fadar Shugaban 'Kasa ta barrantar da kanta daga kalaman Hadimin shugaba Buhari

Kazalika shugaban kasar ya mika godiyar sa ga gwamnatin kasar Birtaniya dangane da goyon baya gami da gudunmuwar ga Najeriya akan harkokin tsaro da kuma yakar ta'addanci a yankin Arewa maso Gabashin kasar nan gami da inganta harkokin kasuwanci tsakanin kasashen biyu.

A na ta jawaban, Firai Ministar ta yi farin cikin kasancewar ta a birnin Abuja inda suka tattauna da shugaba Buhari musamman kan harkokin tsaro, kasuwanci, yaki da cin hanci da rashawa da kuma dawowa da Najeriya kudaden da gwamnatocin baya suka wawushe.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit

Mailfire view pixel