Yan sanda sun kama wani jami’in soja kan harbin wani mai mota

Yan sanda sun kama wani jami’in soja kan harbin wani mai mota

- Yan sanda sun kama wani jami’in kwastam a yankin Badagry

- Hakan ya biyo bayan harbin wani mai mota da kwatam din yayi

- Kakakin rundunar kwastam na Seme Border yace basu da labarin lamarin tukuna

Yan sanda sun kama wani jami’in kwastam kan laifin harbin wani mai mota a tashar Iya-Afin Badagry a ranar Laraba, 29 ga watan Agusta.

Majiyoyin yan sanda sun bayyanawa kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a Badagry cewa jami’in kwastam din wanda aka boye sunansa ya harbi wani mutum a kafadarsa na dama saboda yaki tsayawa a bincike shi.

A cewar majiya, mai motan wanda ke fitowa daga Seme Border, yaki tsayawa a inda ake duba motoci don haka sai jami’in ya bude masa wuta inda abun ya same shi a kafadarsa na dama.

Yan sanda sun kama wani jami’in soja kan harbin wani mai mota

Yan sanda sun kama wani jami’in soja kan harbin wani mai mota
Source: Depositphotos

Don haka wani babban jami’in dan sanda Samson Akinromen dake sashin yan sandan Badagry ya ziyarci wajen da abun ya faru a take sannan yayi umurnin kama jami’in kwastam din.

Majiyar ta kara da cewa wasu yan uwan wanda abun ya shafa da suka ziyarci ofishin yan sandan sai aka sanar da su cewa an mika lamarin zuwa ga yan sandan yankin “K” dake Morogbo.

KU KARANTA KUMA: Zan kashe kaina idan Buhari ya fadi a zaben 2019 – Wani mutumin Abuja yayi barazana

Kakakin kwatam din Seme Border, Saidu Abdullahi ya fadama NAN cewa ba’a kawo masu rahoton lamarin ba tukuna.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel